Tinubu Ya Kori Manyan Shugabannin Hukumomi 4, Ya Maye Gurbinsu Nan Take

Tinubu Ya Kori Manyan Shugabannin Hukumomi 4, Ya Maye Gurbinsu Nan Take

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi sabbin nade-nade inda ya sallami shugabannin hukumomin FAAN da NAMA
  • Tinubu ya kori Kabir Mohammed a matsayin shugaban hukumar FAAN inda ya maye gurbinsa da Olabunmi Kuku
  • Shugaban ya kuma sallami Tayyib Odunowo a matsayin shugaban hukumar NAMA tare da nada Umar Farouk a madadinsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Shugaba Tinubu ya sallami shugaban Hukumar Kula da Jiragen Sama (FAAN), Kabir Mohammed.

Shugaban ya kuma kori Tayyib Adetunji Odunowo a matsayin shugaban hukumar NAMA, cewar TheCable.

Tinubu ya sallami shugabannin hukumomin FAAN, NAMA
Tinubu ya sake sabbin nade-nade a hukumomin FAAN, NAMA. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Yaushe Tinubu ya yi sabbin nade-naden?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Laraba 13 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Kasa da awa 24 bayan Tinubu ya kori shugabannin hukumomi, ya sake korar daraktocin da Buhari ya nada

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ngelale ya ce Tinubu ya nada Olabunmi Kuku a matsayin wanda zai maye gurbin Kabir a hukumar FAAN.

Har ila yau, shugaban ya nada Umar Farouk a matsayin wanda zai maye gurbin Odunowo a hukumar NAMA.

Sabbin nade-naden za su fara aiki ne nan take kamar yadda sanarwa ta tabbatar, Legit ta tattaro.

Sauran wadanda aka sallama a hukumominsu

Sanarwar ta ce:

"Shugaba Tinubu ya amince da dakatarwa da sallama da kuma nadin shugabannin wadannan hukumomi da ke ma'aikatar kula da jiragen sama."

Shugaban ya kuma amince da nadin Alex Badeh Junior a matsayin shugaban hukumar NSIB bayan ya sallami Akinola Olateru a matsayin shugaban hukumar.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Tinubu ya sallami shugaban hukumar NIMET, Mansur Bako Matazu inda ya maye gurbinsa da Charles Anosike a matsayin babban daraktan hukumar.

Kara karanta wannan

Babban magana: Obasanjo ya nemi bayar da shaida kan tsohon ministan da EFCC ke nema ruwa a jallo

Tinubu ya shiga tsakani a rikicin Ondo

A wani labarin, Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sake shiga tsakani kan rikicn siyasa a jihar Ondo da ta ki ci ta ki cinyewa.

Wannan shi ne karo na biyu da shugaban ke saka baki amma a karon farko da ya shiga ba a samu abin da ake bukata ba.

Wannan na zuwa ne yayin da rikicin siyasar jihar ke kara kamari a jihar tun bayan rashin lafiyar Gwamna Rotimi Akeredolu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel