Kasa da Awa 24 Bayan Tinubu Ya Kori Shugabannin Hukumomi, Ya Sake Korar Daraktocin da Buhari Ya Nada

Kasa da Awa 24 Bayan Tinubu Ya Kori Shugabannin Hukumomi, Ya Sake Korar Daraktocin da Buhari Ya Nada

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sake sallamar dukkan daraktocin da ke ma'aikatar kula da harkokin jiragen sama
  • Wannan na zuwa ne kasa da awa 24 bayan Tinubu ya sallami shugabannin hukumomin FAAN da NAMA a jiya
  • Ma'aikatar kula da harkokin jiragen sama ita ta bayyana haka ta bakin kakakinta, Odutayo Oluseyi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kasa da awanni 24 da korar shuagabannin hukumomin jiragen sama, Tinubu ya kori dukkan daraktocinsu.

A jiya ne Shugaba Tinubu ya sallami shugabannin hukumomin FAAN da NAMA tare da maye gurbinsu, cewar The Nation.

Tinubu ya sake sallamar dukkan daraktocin ma'aikatar harakokin jiragen sama
Tinubu ya kori daraktocin ma'aikatar kula da jiragen sama. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Yaushe Tinubu ya sallami daraktocin a ma'aikatar?

Ma'aikatar kula da harkokin jiragen sama ita ta bayyana haka ta bakin kakakinta, Odutayo Oluseyi inda ya ce an sallami dukkan daraktocin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kori manyan shugabannin hukumomi 4, ya maye gurbinsu nan take

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An umurci wadanda abin ya shafa su mika dukkan abin da ke tare da su ga manyan ma'aikatan ofisoshinsu.

Daily Trust ta tattaro cewa wasu daga cikin daraktocin an nada su ne kwanaki kadan kafin rantsar da Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

Wasu daraktoci Tinubu ya sallama a yau?

Wannan na zuwa ne bayan shugaban ya kori shugabannin hukumomin FAAN da NAMA da NSIB da NIMET da sauransu sa ke karkashin ma'aikatar kula da harkokin jiragen sama a kasar.

Daga cikin daraktocin da abin ya shafa sun hada da:

1. Daraktan hukumar FAAN

2. Daraktan hukumar NiMET

3. Daraktan hukumar NAMA

4. Daraktan hukumar NCAA

5. Daraktan hukumar NSIB

Sanarwar ta ce:

"An tabbatar min da cewa dukkan sakatarori da masu ba da shawara a bangaren shari'a abin bai shafe su ba.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Shugaba Tinubu ya umarci majalisar ta miƙa mulki ga mataimakin gwamnan APC

"Dukkan daraktocin da abin ya shafa an roke su da su bi umarni."

Tinubu ya sallami shugabannin FAAN, NAMA

A wani labarin, Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sallami shugabannin hukumomin FAAN da NAMA da wasu daban.

Tinubu ya kori Mohammed Kabir a matsayin shugaban FAAN tare da maye gurbinsa da

Har ila yau, shugaban ya sallami shugaban hukumar NAMA, Tayyib Odunowo yayin da ya maye gurbinsa da Umar Farouk nan take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel