Yanzu: Tinubu Ya Umurci Majalisar Ondo Ta Mika Mulki Ga Mataimakin Gwamna, Aiyedatiwa

Yanzu: Tinubu Ya Umurci Majalisar Ondo Ta Mika Mulki Ga Mataimakin Gwamna, Aiyedatiwa

  • Shugaban kasa Tinubu ya nuna damuwa game da halin rashin lafiya da Rotimi Akeredolu ke ciki sannan ya bukaci a mika mulki ga mataimakinsa
  • A cewar Tinubu, lafiyar Akeredolu na kara tabarbarewa ta yadda ba zai iya sanya hannu kan takardu ba
  • Domin samun mafita mai dorewa kan rigingimun da ke faruwa a jihar, ya umarci majalisa da ta ba Lucky Aiyedatiwa damar jagoranci domi Akeredolu ya mayar da hankali kan lafiyarsa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Shugaban kasa Bola Tinubu ya umurci majalisar dokokin Ondo, da ta mika mulki ga mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa.

An rahoto cewa Tinubu ya bayyana hakan ne a taron da ya kira domin magance rikicin shugabanci a Ondo a ranar Litinin, 12 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Ondo: Jikin Gwamna Akeredolu ya tsananta, ya mika mulki hannun mataimakinsa, ya tafi neman magani

Tinubu ya raba gardama a rikicin Ondo
Yanzu: Tinubu Ya Umurci Majalisar Ondo Ta Mika Mulki Ga Mataimakin Gwamna, Aiyedatiwa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Shugaban kasar ya jaddada cewa a gudanar da shirin mika wannan mulki ba tare da wani sharadi ba, domin ya yi dai-dai da tsarin doka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Nation ta rahoto cewa za a mika mulkin ne ta hanyar sanya hannu ta na'ura saboda gwamnan da ke fama da rashin lafiya ba zai iya sanya hannu kan wata takarda ba.

Wannan matakin zai bai wa Gwamna Akeredolu damar yin hutun jinya, tare da tabbatar da lafiyarsa, Sahara Reporters ta tabbatar.

Tinubu ya sammaci yan majalisar Ondo

A baya mun ji cewa Shugaba Tinubu ya sake shiga lamarin rikicin siyasa ta ke kara kamari a jihar Ondo.

A jiya Litinin 11 ga watan Disamba, Tinubu ya sake gayyatar mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa da kakakin Majalisar, Olamide Oladiji.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Gobara ta kama ofishin gwamnan jihar Borno

Wannan na zuwa ne bayan Tinubu ya shiga tsakani a rikicin siyasa da ta addabi jihar saboda yadda Gwamna Rotimi Akeredolu ya zama a jihar. Rotimi Akeredolu ya gagara zama a jihar.

Jikin Akeredolu ya yi tsanani

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya sanar da daukar hutu a ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, 2023 don zuwa neman lafiyarsa.

Da wannan ne Akeredolu ya mika rikon mulkin jihar hannun mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa har zuwa lokacin da zai samu cikakkiyar lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel