Magidanci Ya Yi Kokarin Salwantar da Ran Matarsa Kan Abu 1

Magidanci Ya Yi Kokarin Salwantar da Ran Matarsa Kan Abu 1

  • Wani magidanci a jihar Bauchi ya yi yunƙurin halaka matarsa domin samun ƙara kuɗin jari a shagonsa
  • Magidancin wanda ɗan kasuwa ne ya yi yunƙurin halaka matar ne domin ya sayar da talabijin ɗinsu
  • Rundunar ƴan sandan jihar wacce ta tabbatar da aukuwar ta ce magidancin yana hamnu kuma ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Wani magidanci ya shiga hannun jami'an tsaro bisa yunƙurin kashe matarsa a jihar Bauchi.

Magidancin wanda ɗan kasuwa ne dai ya yi yunƙurin halaka matar tasa ne domin ya sayar da talabijin ɗinsu ya ƙara jari a shagonsa, cewar rahoton Aminiya.

Magidanci ya so halaka matarsa a Bauchi
Magidanci ya yi yunkurin kashe matarsa a Bauchi Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

An yi caraf da magidancin ne bayan ya yi wa matar tasa dukan tsiya da taɓarya da niyyar salwantar da ranta a ranar 2, ga watan Disamban 2023.

Kara karanta wannan

Iyalan dalibin jami'a da ayarin motocin gwamna suka halaka na neman adalci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin ta bayyana cewa magidancin ya bayyanawa masu bincike cewa ya yi niyyar halaka matarsa ne, rahoton The Punch ya tabbatar.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce an kai matar Asibitin Kwararru da ke Bauchi domin kulawa da ita a sakamakon munanan raunukan da mijin ya yi mata da taɓaryar.

Yadda lamarin ya auku

Kakakin ya kuma bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa tuhumar da ake yi masa ba tare da wata jayayya ba.

A kalamansa:

“Ya yi iƙirarin cewa ya yi mata ƙaryar cewa ƴan fashi sun shiga gidansu, shi ne ya shiga ɗakin da suke kwance ​​ya ce mata ta rufe kanta da gyale."
"Sai ya fita ya je ya rufe fuskarsa da mayafi, sannan ya ɗauko taɓarya ya dawo ɗakin ya fara dukanta da ita."

Kara karanta wannan

An shiga jimami yayin da ramin hakar ma'adanai ya rufta kan mutane a jihar Arewa

Kakakin ya ƙara da cewa kwamishinan ƴan sandan ijhar, Auwal Mohammed, ya bayar da umarnin miƙa wanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuka domin zurfafa bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu da zaran an kammala bincike.

Dan Najeriya Ya Halaka Matarsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ɗan Najeriya da ke zaune a ƙasar Burtaniya ya salwantar da ran matarsa.

Ƴan sanda sun yi caraf da David Olubunmi Abodunde mai shekara 47 da laifin kashe matarsa, Taiwo Owoeye Abodunde, wacce ma'aikaciyar jinya ce a Suffolk, Burtaniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel