Dattijo Dan Shekara 84 Ya Halaka Matarsa Yar Shekara 75 Kan Hana Shi Hakkin Aure

Dattijo Dan Shekara 84 Ya Halaka Matarsa Yar Shekara 75 Kan Hana Shi Hakkin Aure

  • Wani dattijo mai shekaru 84, ya aika da matarsa mai kimanin shekaru 75 lahira
  • Dattijon ya bayyana cewa matar ta sa ba ta ba shi hakkinsa na kwanciyar aure, a yayinda take mu'amala da wasu a waje
  • Sai dai dattijon ya ce ya yi nadamar abinda ya aikata, wanda ya yi a cikin tsananin fushin da ya samu kansa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Edo - Wani dattijo mai shekaru 84 mai suna Gabriel Uhuwa, ya bayyana cewa shi ne ya kashe matarsa mai kimanin shekaru 75 a duniya.

Ya bayyana cewa ba ta yadda ta kwanta da shi, kuma labari ya iske shi cewa tana kwanciya da wasu Fastoci kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Miji ya halaka matarsa yar shekara 75 a jihar Edo
Dattijo dan shekara 84 ya halaka matarsa yar shekara 75 a jihar Edo. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Dattijon ya halaka matarsa kan hana shi hakkin aure

Gabriel dai na cikin mutane 198 da rundunar 'yan sandan jihar Edo ta gurfanar bisa tuhume-tuhume kan laifuffukan da suka shafi fashi da makami, garkuwa, mallakar makamai da sauransu.

Kara karanta wannan

Yadda Saurayi Ya Rabu Da Budurwarsa Saboda Ta Yi Yunkurin Shiga Kundin Bajinta Na Guinness, Ya Ce Ta Kunyata Shi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake zantawa da manema labarai, dattijon wanda mahaifi ne ga 'ya'ya bakwai, ya bayyana cewa an kwashi tsawon lokaci ba tare da matar ta sa ta yarda ta kwanta da shi ba.

Ya ce a dalilin hakan ne ya yanke shawarar kasheta duk da dai a yanzu ya yi nadamar abinda ya aikata kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

Yadda ɗan shekara 84 ya halaka matarsa mai shekaru 75

Gabriel ya bayyana cewa, matar tasa ba ta yi ma sa biyayya kwata-kwata a duk lokacin da ya nuna yana da bukatarta.

Ya ce sun haifi yara bakwai tare da ita; maza biyar da kuma mata biyu, wanda har wajen 'ya'yan na ta sai da ya kai ƙararta dangane da lamarin, amma kuma duk da haka ba ta daina abinda take ba.

Kara karanta wannan

Malamar Makaranta Ta Sharbawa Daliba Zane 4 a Fuska, Mahaifiyar Yarinyar Ta Saki Hotuna

Ya ƙara da cewa a duk lokacin da ya buƙace ta sai ta ce ma sa ba ta da lafiya, ko ta yi ƙaryar cewa ciwon gyambon ciki na damunta, amma kuma ya samu labarin cewa tana mu'amala da wasu.

A ranar Asabar ɗin makon da ya gabata ne dai Gabriel ya gaza haƙuri, inda ya yi amfani da wata adda wajen aika matar ta sa barzahu da ita.

Mata ta nemi saki a kotu saboda mijin ya gaza ciyar da ita

Legit.ng a baya ta yi wani rahoto, kan wata mata da ta shigar da mijinta ƙara a gaban kotu, inda ta nemi a raba aurenta da shi.

Matar ta koka kan yadda mijin na ta yake gaza ciyar da ita da kuma ba ta 'yan kuɗaɗen da za ta yi amfani da su wajen kula da kanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel