Iyalan Dalibin Jami'ar da Ayarin Motocin Gwamna Suka Halaka Na Neman A Yi Musu Adalci

Iyalan Dalibin Jami'ar da Ayarin Motocin Gwamna Suka Halaka Na Neman A Yi Musu Adalci

  • Rahotanni sun ce ayarin motocin gwamnan jihar Ebonyi sun halaka wani ɗalibin jami’ar jihar Ebonyi har lahira
  • An tattaro cewa a lokacin da lamarin ya auku, Gwamna Francis Nwifuru baya cikin ayarin motocin
  • Iyalan mamacin dai na neman a yi musu adalci yayin da suke zargin rundunar ƴan sandan jihar Ebonyi da ɓoye shaidu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Abakaliki, Ebonyi - Iyalan wani ɗalibi, Ebube Akah, dake jami’ar jihar Ebonyi, na neman a yi musu adalci, bayan da ɗalibin da wani ɗan Achaɓa suka mutu a wani hatsarin mota da ya ritsa da ayarin motocin Gwamna Francis Nwifuru a makon jiya.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 1 ga watan Disamba, a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, amma rahotanni sun ce gwamnan ba ya cikin ayarin motocin a lokacin.

Kara karanta wannan

An kuma: Yan bindiga sun kai sabon hari, sun yi garkuwa da ɗaliban jami'ar tarayya a arewa

Ayarin motocin Nwifuru sun halaka dalibi
Ana zargin yan sanda da yin rufa-rufa kan kisan da aka yi wa dalibin Hoto: Gov Francis Nwifuru
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, babban yayan Ebube, Isidore Akah, ya zargi ƴan sandan da yin rufa-rufa a kan lamarin, ya kuma yi iƙirarin cewa ƴan sandan ba su ɗauki wani mataki ba duk da ganawar da suka yi da kwamishinan ƴan sandan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Ayarin motocin gwamnan da suka je makaranta domin ɗauko yaran gwamnan, ta buge Ebube da ɗan Achaɓa kuma dukkansu sun mutu nan take."

Rundunar ƴan sandan ta tabbatar da aukuwar lamarin amma ba ta yi magana kan zarge-zargen ba. Har yanzu Gwamna Nwifuru da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai ba su amsa tambayoyi ba.

Ya zargi ƴan sanda da cire layukan waya daga wayar Ebube don hana magana da ƴan'uwansa.

Yadda hatsarin ya auku

Akah ya bayyana cewa a ranar Juma’a, 1 ga watan Disamba, Ebube ya tashi daga gida domin ɗauko wani abu a kan titin Afikpo ta hanyar Onwe a cikin babban birnin Abakaliki.

Kara karanta wannan

An tsinci gawar budurwa a dakin otel bayan sun je holewa da saurayinta, yan sanda sun dauki mataki

Sai dai abin takaicin shi ne, lamarin ya faru ne yayin da babur din da yake a kai ya yi karo da wata mota a cikin ayarin motocin Mista Nwifuru, da ke kan hanyar daukar yaran gwamnan daga makaranta.

Ebube da ɗan Achaɓan da aka fi sani da Sharhabilu daga jihar Zamfara sun rasa rayukansu a wurin da hatsarin ya afku.

Ya ƙara da cewa, ƴan kallo sun yi ca kan ɗaya daga cikin direbobin da ke da hannu a hatsarin, amma jami’an tsaro suka shiga tsakani suka cece shi daga hannunsu.

Iyalin waɗanda suke cikin baƙin ciki, sun gano gawar Ebube a ɗakin ajiyar gawa kwana biyu bayan bincike mai zurfi.

Yayin da gawar Ebube ke ci gaba da zama a dakin ajiye gawa, an yi jana’izar ɗan Achaɓan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a Abakaliki.

Matafiya Sun Ƙone a Hatsarin Mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu matafiya tara cikin 13 sun samu raunukan ƙuna daban-daban a lokacin da motarsu ta yi karo da wata tirela a kan hanyar Ogbomoso zuwa Oyo a jihar Oyo.

Kwamandan hukumar FRSC reshen Oyo, Joshua Adekanye ya ce hatsarin ya haɗa da wata tirela da wata babbar mota a unguwar Sekona da ke kan titin Ogbomoso zuwa Oyo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel