An Shiga Jimamai Yayin da Ramin Hakar Ma'adanai Ya Rufta Kan Mutane a Jihar Arewa

An Shiga Jimamai Yayin da Ramin Hakar Ma'adanai Ya Rufta Kan Mutane a Jihar Arewa

  • Rayukan mutum uku sun salwanta bayan wani ramin haƙar ma'adanai ya rufto kan ma'aikata a Zamfara
  • Ramin wanda ya rufto a ƙaramar hukumar Anka ta jihar ya kuma yi sanadiyyar jikkata rayukan mutum 11
  • Ganau ba jiyau ba sun tabbatar da cewa ba a san adadin yawan mutanen da suke cikin ramin ba lokacin da lamarin ya auku

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Aƙalla masu aikin haƙar ma'adanai mutum uku ne suka rasu yayin da wasu mutum 11 suka samu raunuka sakamakon ruftawar wani ramin haƙar ma'adinai a Dan Kamfani da ke ƙaramar hukumar Anka ta jihar Zamfara.

A cewar wani ganau da ke aiki a kewayen yankin, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 4 na yamma, cewar rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

An kuma: Yan bindiga sun kai sabon hari, sun yi garkuwa da ɗaliban jami'ar tarayya a arewa

Masu hakar ma'adanai sun rasu a Zamfara
Mutum uku sun rasu wajen hakar ma'adanai a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Wani ganau wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro a ranar Asabar ya bayyana cewa an tabbatar da rasuwar wasu masu aikin haƙar ma’adanai mutum uku yayin da wasu mutum 11 suka samu munanan raunuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce a halin yanzu waɗanda suka jikkata suna samun kulawa a babban asibitin Anka.

A kalamansa:

"Ramin haƙar ma'adanan ya ruguje ne ƴan mintuna kafin ƙarfe hudu na yammacin ranar Alhamis, ba mu san adadin mutanen da ke cikin ramin hakar ma'adinan ba, amma an gano gawarwaki uku, wasu mutum 11 kuma sun samu munanan raunuka."
"Mutane ukun da suka rasu sun fito ne daga gundumar Yar Tsabaya ta ƙaramar hukumar Anka. Ya zuwa yanzu, ba mu da ainihin adadin mutanen da ke ciki, kuma ba za mu iya tabbatar da adadin mutanen ba saboda ramin ya kai zurfin mita 275."

Kara karanta wannan

Ana cikin jimamin masu maulidi yan bindiga sun halaka mutum 33 a wani sabon hari

An haramta haƙar ma'adanai a Zamfara

Zamfara tana da wadataccen ma'adanai da suka hada da zinare, tama, farar ƙasa, da granite da dai sauransu.

Gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar sun haramta duk wani nau'i na ayyukan haƙar ma'adinai tare da umartar hukumomin tsaro da su aiwatar da dokar.

Mafi yawa daga cikin masu aikin haƙar ma'adanai da ke a jihar suna aiki ne ba tare da lasisi ba.

Rami Ya Rufta da Masu Hakar Ma'adanai

A wani labarin kuma, kun ji cewa Mutane uku sun mutu bayan da wata mahakar ma'adanai da suke aiki a ciki ta rufta a yankin Anyiin da ke karamar hukumar Logo a jihar Benue.

An tattaro cewa marigayan sun kasance suna cikin haƙo ne lokacin da ramin ya rufta dasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel