Mahara Sun Bukaci Miliyan 53 Kudin Fansar Malamin Addini da Wasu Mutum 2 a Jihar Arewa

Mahara Sun Bukaci Miliyan 53 Kudin Fansar Malamin Addini da Wasu Mutum 2 a Jihar Arewa

  • Kwanaki kadan bayan sace shahararren Fasto da wasu mutane biyu a Kwara, maharan sun bukaci kudin fansa miliyan 53
  • Dagacin kauyen Agbeku, Oba Abdulazeez Shola shi ya tabbatar da haka ga manema labarai inda ya ce an fara bincike kan lamarin
  • Idan ba a mantaba, a ranar Asabar ce 11 ga watan Nuwamba ‘yan bindigan suka sace Faston da wasu mutane biyu a jihar Kwara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara – Masu garkuwa da su ka sace Fasto da wasu mutane biyu sun bukaci kudin fansa har naira miliyan 53.

Maharan sun sace mutanen uku ne a karamar hukumar Ifelodun da ke jihar Kwara a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba, cewar Trust Radio.

Kara karanta wannan

Ruguntsumi yayin da NLC ta garkame mambobin Majalisar Tarayya a Abuja, ta yi abu daya

Mahara sun bukaci miliyan 50 kudin fansar malamin addini a Kwara
A karshe, masu garkuwa sun bayyana kudin fansar Fasto a Kwara. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Su waye maharani suka sace a jihar Kwara?

Daga cikin wadanda aka sacen akwai Rabaran S. B Oladunni wanda shi ne shugaban cocin Igabala DCC da kuma wasu mutum biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai sarautar gargajiya na Agbekuland, Oba Abdulazeez Shola ya tabbatar da sanarwar kudin fansar a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba ga manema labarai.

Ya ce rundunar ‘yan sanda a jihar ta fara bincike kan lamarin don samun bayanai da kuma dakile faruwar hakan a gaba.

Na wa maharan ke bukata na kudin fansa?

Ya ce:

“Yayin da aka gindaya miliyan 20 kan Faston, miliyan 30 ne daya matar za ta biya yayin da mutum na ukun zai biya miliyan 3.”

Daily Trust ta tabbatar cewa jami’an ‘yan sanda sun cafke wasu mutane uku da ake zargi da hannu a cikin satar mutanen a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da mahara suka yi garkuwa da Farfesa a Jami'a, 'yan sanda sun yi martani

Mahara sun yi garkuwa da Fasto a jihar Kwara

A wani labarain, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shahararren Fasto da wasu mutane biyu a jihar Kwara a karshen makon nan.

Maharan sun sace mutanen ne a kauyen Agbeku da ke karamar hukumar Ifelodun da ke jihar Kwara a ranar Asabar da ta gabata.

Rundunar ‘yan sanda a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce ta baza jami’anta lungu da sako din ceto mutanen da aka sacen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel