Tashin Hankali Yayin da Mahara Suka Yi Garkuwa da Farfesa a Jami'a, 'Yan Sanda Sun Yi Martani

Tashin Hankali Yayin da Mahara Suka Yi Garkuwa da Farfesa a Jami'a, 'Yan Sanda Sun Yi Martani

  • Mahara sun yi garkuwa da wani Farfesa a Jami'ar Calabar da ke jihar Kuros Riba a Kudancin Najeriya
  • Farfesa Patrick Egaga ya shiga hannun maharan ne a daren jiya Lahadi 12 ga watan Nuwamba a gidansa da ke rukunin gidajen ma'aikatan Jami'ar
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, SP Irene Ugbo ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce sun bazama ceto Farfesan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kuros Riba - 'Yan bindiga sun sace daraktan 'Servicom' a Jami'ar Calabar da ke jihar Kuros Riba.

Maharan sun sace Farfesa Patrick Egaga ne a daren jiya Lahadi 12 ga watan Nuwamba a gidajen ma'aikatan Jami'ar, cewar Vanguard.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da Farfesa a Jami'ar Calabar
'Yan sanda sun bazama ceto Farfesan da ka yi garkuwa da shi. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Yaushe aka sace Farfesan a Jami'ar Calabar?

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan wasu ‘yan bindiga sun bindige shugaban jam’iyyar siyasa a jihar Anambra

Egaga wanda Farfesa ne a tsangayar ilimi ta musamman a Jami'ar an tabbatar da garkuwa da shi a cikin gidansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, SP Irene Ugbo ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Litinin 13 ga watan Nuwamba.

Irene ya ce duk da iyalan Farfesan ba su kawo rahoton garkuwa da shi ba, amma rundunar ta bazama nemanshi, The Guardian ta tattaro.

Kakakin rundunar a jihar ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a Calabar babban birnin jihar Kuros Riba.

Wane martani hukumar makarantar ta yi kan garkuwar?

Har ila yau, kakakin Jami'ar, Mista Effiong Eyo ya ce sun samu labarin garkuwa da Farfesan ne a yau Litinin 13 ga watan Nuwamba.

Punch ta tattaro cewa maharan sun tsere da Farfesa ne ta cikin kogi da ya ke kusa da gidan ma'aikatan Jami'ar.

Kara karanta wannan

Dakarun soji sun damke wasu motoci 3 da ake zargi a zaben jihar Kogi

Har ila yau, an tabbatar da cewa maharan sun zo ne ta kogin wanda ya hada birnin Calabar da karamar hukumar Akpabuyo da ke jihar.

'Yan sanda sun cafke mata kan cin zarafin mijinta

A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Ribas ta cafke wata mata da zargin watsa wa mijinta tafasasshen man gyada.

Matar mai suna Hope ta aikata wannan danyen aiki ne yayin da mijin nata ke sheka barci a daki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel