Murja Kunya Ta Gargadi Masu Gigin Soyayya, Ta Fadi Babban Abin Da Ya Hana Ta Aure

Murja Kunya Ta Gargadi Masu Gigin Soyayya, Ta Fadi Babban Abin Da Ya Hana Ta Aure

  • Murja Ibrahim Kunya ta ce ba komai ya hana ta yin aure ba sai wasu manya-manyan bakaken aljanu da ta ke fama da su
  • ‘Yar Tik Tok din ta sanar da masu neman ta da soyayya su san aikin da su ke neman barowa kan su kafin tafiya ta yi nisa
  • Hajiya Murja Kunya ta fahimci Hukumar Hisbah ta na kokarin yi mata aure ne, ita kuma ta nuna zama gidan miji zai yi wahala

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Da alama akwai aiki a gaban hukumar Hisbah ta jihar Kano domin Murja Ibrahim Kunya ta nuna ba ta da niyyar yin aure.

A wani bidiyo da mu ka ci karo da shi a dandalin Facebook, Murja Ibrahim Kunya ta bayyana cewa bakaken aljanu su ka hana ta aure.

Kara karanta wannan

Kudin litar man Fetur zai iya saukowa saboda faduwar farashin ganga a Duniya

Dr. Muhammad Hashim Sulaiman ya wallafa wannan bidiyo a shafinsa a safiyar Laraba.

Murja Kunya
Ana son aurar da Murja Ibrahim Kunya Hoto: Crypto Love
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Murja Kunya da maganar aure

Wannan Baiwar Allah da ta shahara a kafar Tik Tok ta ankarar da manemanta cewa idan aka zo mata da batun aure, ta na gwabje mutane.

"Ni fa na fahimci mutanen nan so su ke yi su aurar da ni, kuma babu wani kure-mure, wallahi aljanu ne a jiki na.
Manya-manyan bakaken aljanu ne. Ni ma ni kadai wani lokaci sai in hau naushe-naushe, ko ku ga ina fizge-fizge."

- Murja Ibrahim Kunya

Murja Kunya ta na gwabje manema

Murja Kunya ta ce abin na ta ya fi kamari ne a cikin dare, a sanadiyyar haka ne wani maneminta da ya zo zance, ya yabawa aya zakinta.

A cewarta, tun da wannan ta’aliki ya yi subutar baki ya fada mata ya na kaunar ta, da ta yi masa wani kutufo, sai dai aka gano shi a wani jeji.

Kara karanta wannan

A shirya: Fadar Shugaban Kasa ta fadi mamayar da Tinubu zai yi wa 'yan boye dala

A bidiyon, an ji Murja Kunya ta na cewa watakila aljanun tsohon masoyinta ne su ka dawo jikinta bayan rasuwarsa, su ke neman hana ta aure.

Mai auren Murja sai 'dan dambe

"Da ka yi mani zancen aure sai kutufo, amma duk wanda ya ga zai diba a haka, babu damuwa ka diba, amma ka tabbatar kai ‘dan dambe ne.
Haka na ke kuma ni ma ban san ina kai harin ba, sai idan na gama ragargazar mutum na ke sani.
Haka kurum duka na ke yi, ina kuma ga a ce an makure ni da karfi da yaji, an cusa a dakin miji?"

- Murja Ibrahim Kunya

An yi wa Murja Kunya duka?

Kwanaki aka yi ta yawo da labari cewa wasu matasa da ba a san ko su wanene ba sun yi wa jarumar ta TikTok dukan tsiya a garin Kano.

Ana zargin matasan da su ka yi wannan zalunci sun sauyawa Murja kamanni. An yi kira ga jami’an tsaro su yi bincike domin a hukunta su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng