Abba Gida-Gida Zai Yi Wa Murja Kunya Sakayya, Zai Yi Mata Aure Daga Cikin Zaurawan Da Zai Aurar

Abba Gida-Gida Zai Yi Wa Murja Kunya Sakayya, Zai Yi Mata Aure Daga Cikin Zaurawan Da Zai Aurar

  • Gwamnan jihar Kano ya bayyana aniyarsa na aurar da Murja Kunya a shirin auren zaurawa da gwamnatinsa ta tsara a jihar
  • A cewarsa, ta yi kokari wajen tabbatar da gwamnatinsa ta kafu, don haka za a yi mata sakayya da alherin aure sunnar ma’aiki
  • Gwamnatin Kano ta ware kudade da dama domin yiwa zaurawa aure a jihar, inda tuni aka fara shirin yadda hakan za ta kasance

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Fitacciyar ‘yar TikTok, Murja Kunya za ta amarce a auren zaurawa da za a gudanar nan ba da jimawa ba a jihar Kano.

Wannan na fitowa ne daga bakin gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida-Gida yayin da yake jawabi, Aminiya ta ruwaito.

Da yake bayani a gidan gwamnatin Kano, Abba gida-Gida ya ce zai aurar da Murja a shirinsa na aurar da zaurawa da za a yi a jihar don raya sunnah.

Kara karanta wannan

"Gobe Ka Kara": Matar Aure Ta Kwarawa Dan Cikinta Tafasashshen Ruwan Zafi Bayan Ya Aikata Wani Abu 1

Za a yiwa Murja Ibrahim Aure
Abba Gida-Gida zai aurar da Murja 'yar TolTok | Hoto: Murja Ibrahim Kunya
Asali: TikTok

Dalilin da yasa zai aurar da Murja

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Abba, aurar da Murja zai zama yi mata sakayya da irin gudunmawa da kokarin da ta yi wajen kafuwar gwamnatinsa a watan Maris din bana.

Ga dai abin da Abba ke cewa:

“Kowa ya san irin rawar da Murja ta taka wajen yayata ayyukan alheri da gwamnatin nan ke yi, wanda babu abin da za mu ce sai son barka.
“Kuma ita ce ta fara fitowa a cikin ’yan tawagarsu [’yan TikTok] ta ce tana son a yi mata aure sunnar Manzon Allah.
“Matar da ta fito ta ce tana son a inganta sunnah ta Manzon Allah ai ba a bar kyama bace.
“Kuma so take ta je inda za ta ba da gudunmawar inganta addinin Musulunci.”

Murja dai na daga cikin wadanda ke yawan jawo cece-kuce a kafar sada zumunta ta TikTok, inda kullum take cikin mayar da martani ga masu sukarta.

Kara karanta wannan

Ya za a yi? Davido ya ce kudi ne matsalar Najeriya, ya ba da shawarin mafita

Mazan da matan Kwankwasiyya ke hange

A tun farko, zaurawan Kwankwasiyya sun kyallaro ido sun hangi irin wadanda suke so a aura musu a auren zaurawa da za a yi.

An tattauna da daya daga cikinsu, inda ta bayyana mazan da suke so su amarce da su a auren da a gudanar.

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin Abba Gida-Gida ta sanar da fara yin auren zaurawan nan ba da jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel