Na Daina Nuna Rashin Tarbiya a Soshiyal Midiya, Murja Ibrahim Kunya

Na Daina Nuna Rashin Tarbiya a Soshiyal Midiya, Murja Ibrahim Kunya

  • Murja Ibrahim Kunya ta sha alwashin daina yin zage-zage da duk wasu dabi'un rashin tarbiya a soshiyal midiya
  • Yan sanda dai sun kama Murja bayan wasu lauyoyi da malamai sun yi kararta bisa zarginta da lalata tarbiya
  • Jarumar ta TikTok ta bayyana dalilanta na yin zage-zage ciki harda jita-jitan da aka dunga yadawa cewa ta mutu

Kano - Shahararriyar jarumar nan mai nishadantar da jama'a a TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta sha alwashin cewa daga yanzu ta daina zage-zage a shafukan soshiyal midiya.

Murja wacce ta kasance yar asalin jihar Kano ta dauki wannan alkawarin ne yayin da rundunar yan sandan jihar ta hyi ram da ita kan zarginta da ake da yin badala a shafukan sadarwa, Aminiya ta rahoto.

Har ila yau, matashiyar wacce ake shirin gurfanarwa a gaban alkali, ta sanar da yan sanda cewa ita din ta sauke Al-Kur'ani mai girma tana mai zuwa ta yi alkawarin daina zagi.

Kara karanta wannan

"Ba Za Ta Saɓu Ba": Dattawan Arewa Sun Yi Gargadin Kan Shirin Yin Katsalandan A Zaben 2023

Murja Kunya
Na Daina Nuna Rashin Tarbiya a Soshiyal Midiya, Murja Ibrahim Kunya Hoto: Aminiya
Asali: UGC

A yayin hirarta da mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna-Kiyawa, Murta ta ce duk mai tunani da hankali ya sani idan yana aikata abun da yake ba daidai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, ta musanta zargin da ake mata na lalata tarbiyyar yara domin a cewarta ita ba waka take yi ba balantana su hau wakarta.

Ta ce:

"Da farko dai ni Murna ba waka nake yi ba balle na ce yara za su iya hawa wakata har ya kai ga lalacewar tarbiyyarsu."

Ba ni ce mutum ta farko da ta hau wakar Cas da War na Ado Gwanja ba

Kan zarginta da hawa wakokin batsa da makamantansu, ta ce ita din ba mutum ba ce mai yawan hawa wakokin batsa.

Ta kuma bayyana cewa sam ita bata san cewa wakar 'Cas' da Ado Gwanja ya yi ya saba ma doka ba wannan ne dalilinta na hawa wakar a manhajar TikTok kuma ba ita ce ta fara yin hakan ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon Dirarriyar Amarya Mai Shekaru 57 da ke Nuna Yarinta, Ta Saka Jar Riga ta Amaren Zamani

Murja ta ci gaba da cewa:

"Har ga Allah ni ban sani cewa wannan waka tasa ta keta doka ba, duba ga yadda na ga mutane suna amfani da ita wakar a TikTok shine ya sanya nima na hau ta."

Har wayau, Murja ta ce ta fara yin kicibis da wakar Ado Gwanja ta 'War' ne a soshiyal midiya kuma kafin ma ita ta hau shi, wasu da dama sun aikata hakan.

Jaridar dai ta rahoto cewa hukumar NBC ta haramta sanya wakokin Cas da War bayan sun tayar da kura sakamakon zargin da ake yi suna yada badala.

Sakamakon wadannan wakokin ne wasu lauyoyi a jihar Kano suka maka Ado Gwanja a kotu bisa zargin cewa yana gurbata tarbiyya.

Dalilina da zage-zage a soshiyal midiya, Murja

Matashiyar ta kuma bayyana cewa ta yi zagin da aka kaita kotu kansa ne tun kafin wannan lokaci, tana mai cewa ta yi su ne a lokacin da aka kama wasu mata da yayansu a wani daji ne.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa na rabu da mijina kuma na auri saurayin 'diyata: Malama Khadija

Ta ce sun fara ne roko a kan a taimaka a kawo masu dauki amma abun ya ci tura har ta kai an far masu da duka lamarin da yasa hankalinta ya tashi har ta fito ta yi wannan zage-zagen.

Bayan nan kuma abu biyu da ya sa ta zagi kamar yadda Murja ta fadi shine lokacin da wani ya daura hotonta ya ce ta mutu.sakamakon hatsari a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Ta ce a lokacin da aka sanar da mahaifiyarta wannan labari sai da ta yanke jiki ta fadi lamarin da yasa ta dauki zafi ta yi zage-zagen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng