Hukumar Hisba Za Ta Aurar da Murja Kunya da Sauran 'Yan TikTok Na Kano

Hukumar Hisba Za Ta Aurar da Murja Kunya da Sauran 'Yan TikTok Na Kano

  • Hukumar Hisbah na ci gaba da aikinta na kokarin tsarkake jihar Kano daga dukkan badala
  • Hisbah karkashin jagorancin Sheikh Aminu Daurawa za ta aurar da Murja Ibrahim Kunya da takwarorinta 'yan TikTok a Kano
  • Baya ga auren gata da gwamnatin Kano za ta yi wa 'yan TikTok din, za a basu jari domin gudanar da harkokin kasuwancinsu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano karkashin jagorancin Sheikh Aminu Daurawa, ta sanar da shirye-shiryenta na yi wa 'yan TikTok a Kano auren gata.

Haka kuma, rundunar tsaron ta addinin musulunci ta sanar da cewar baya ga auren gatan da za a yi masu, gwamnatin jihar za ta ba su tallafi don gudanar da harkokin kasuwancinsu.

Kara karanta wannan

Kano: Hisbah ta yi martani kan aske kan wata budurwa da kwalba, ta fadi matakin da ta dauka a kai

Hukumar Hisbah za ta yi wa 'yan TikTok na Kano auren gata
Hukumar Hisba Za Ta Aurar da Murja Kunya da Sauran 'Yan TikTok Na Kano Hoto: Leadership
Asali: UGC

Hisbah ta kira taro da yan TikTok na Kano

Kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto, an sanar da wannan shirin ne yayin wani taro da hukumar ta gudanar a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa, an kira taron ne domin wayar da kan 'yan TikTok din kan yadda za su inganta dabi'unsu.

Tun da farko an gayyaci Murja Ibrahim Kunya, 'yar TikTok da ta shahara wajen haddasa cece-kuce a jihar Kano, da takwarorinta zuwa hedikwatar hukumar ta Hisbah da ke Kano domin yi musu gyara a ranar Litinin, 6 ga Nuwamba, 2023, da karfe 4:00 na yamma.

Gayyatan wanda mataimakin babban kwamandan Hisbah, Dr Mujahid Aminuddeen ya yi, ya karfafawa wadanda suka halarci taron gwiwar kawo takardun karatu da na kasuwancinsu.

Dalilin kiran taron yan TikTok da Hisbah ta yi a Kano

Kara karanta wannan

Kano: NDLEA ta cafke makafi 3 da ke safarar miyagun kwayoyi, sun fadi yadda su ke jigilar kwayar

Babban makasudin wannan taro ya kasance don ba da gudunmawa ga wadanda suke ra'ayin samun taimako daga gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf.

Yan TikTok da dama sun halarci taron ciken shiga ta mutunci sannan fuskokinsu lullune da Niqabi.

An samu ci gaba a yaki da badala a Kano, Hisbah

Tun farko dai hukumar Hisbah ta ce ta kaddamar da aikinta na “Operation Kau da Badala" domin yakar karuwanci a jihar, News Digest ta rahoto.

Dr Aminuddeen ya nuna jin dadinsa da ci gaban da aka samu, inda ya bayyana cewa sun ci karo da guraren da aka yi niyan yin kame babu kowa, wanda hakan ke nuni da samun nasara a kokarinsu na tsarkakewa da dawo da martabar Musulunci a jihar Kano.

PSC da tubabbun yan daba a Kano

A wani labarin, mun ji cewa hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta ƙasa (PSC), a ranar Alhamis, ta yi ƙarin haske kan ɗaukar, "tubabbun 'yan daba" aikin ɗan sanda a jihar Kano.

PSC ta yi bayanin cewa ta ɗauki matakin ɗaukar 'yan daban da suka tuba ne a wani ɓangaren yunƙurin jami'an yan sanda na kawo karshen aikata laifuka a lungu da saƙo na jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng