Bidiyon Liki Na Fitar Hankali da Aka Yi a Wajen Biki Ya Yadu, Mutane Sun Jigata Yayin Kwashe Kudin

Bidiyon Liki Na Fitar Hankali da Aka Yi a Wajen Biki Ya Yadu, Mutane Sun Jigata Yayin Kwashe Kudin

  • Wani bidiyon TikTok da ya yadu ya nuno jama'a suna kwashewa da jefa bandir-bandir na kudi daga kasa bayan wani taro
  • Alamu sun nuna kasaitaccen biki ne wanda ya samu halartan manyan masu hannu da shuni wadanda suka yi wa sabbin ma'auratan liki na fitar hankali
  • Ma'aikatan da aka daurawa alhakin kwashe kudin daga kasa duk sun jigata yayin da yawan kudin ya girgiza jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wani bidiyon TikTok ya ja hankalin dubban masu kallo, yayin da ya nuno mutane suna kwashewa da tattara kudade masu yawan gaske daga kasa bayan kammala wani babban taro.

Alamu sun nuna taron wani kasaitaccen biki ne aka yi wanda ya samu halartan manyan masu fada aji da masu hannu da shuni da suka bude bakin aljihu suka zazzagawa ma'auratan don taya su murna da san barka.

Kara karanta wannan

An kori ma'aikata da yawa daga aiki a jihar Kaduna kan wasu dalilai masu girma

Mutane na kwashe kudi a kasan wajen taro
Bidiyon Mutane Suna Kwashe Damin Kudi Cike da Gajiya a Wajen Kasaitaccen Biki Ya Girgiza Intanet Hoto: TikTok/@caxxie
Asali: TikTok

Ma'aikatan da aka daurawa alhakin kwashe kudaden daga kasa duk sun jigata saboda yawan damin kudaden da suka barbarzu a gaba daya wajen.

Bidiyon ya nuna tsadaddiyar rayuwa ta kashe kudi da wasu manyan mutane ke yi a kasar inda suka kan fitar da kudi su kashe kamar ruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon a kasa:

Matasa sun yi liki harda daloli

A wani labarin, mun ji cewa ranar Juma’a, 26 ga watan Agustan bara ne dubban jama’a suka shaida daurin aure tsakanin Kabiru Aminu Bayero, dan sarkin Kano Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, da kyakkyawar amaryarsa Aisha Ummaran Kwabo.

Duk a cikin shagalin bikin, an gudanar da wani kasaitaccen liyafar Dina wanda ya samu halartan amarya da ango. Kamar yadda aka saba, yan uwa da abokan sabbin ma'auratan sun yi masu kara wajen kasancewa a taron.

Kara karanta wannan

Zan kore ku, ba zan bari shugabannin hukumomi su jawo Tinubu ya tsige ni ba – Minista

Sabbin ma'aurata sun samu kudi a bikinsu

An kuma yi ruwan kudi inda matasa suka sha likin kudade bandir-bandir ciki harda masu ruwan daloli.

A wani labarin kuma, wani ango da amaryarsa sun nunawa duniya ribar da suka samu a bikinsu.

An gano sabbin ma’auratan suna ta tattara bandir bandir din kudade da suka samu a daren aurensu. Hakan ya sanya wa wasu sha’awar son yin biki don su kwashi nasu rabon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel