'Yar Fim a Najeriya Ta Shiga Hannu Bayan Gano Ta Lika Sabbin Naira a Gidan Biki

'Yar Fim a Najeriya Ta Shiga Hannu Bayan Gano Ta Lika Sabbin Naira a Gidan Biki

  • Wata mata a Najeriya ta yi aikin dana-sani yayin da ta lika sabbin Naira a bainar jama'a a gidan biki
  • Labarin da muke samu ya bayyana yadda hukumar EFCC ta kama matar tare da fara in bincike a kanta
  • Ana ci gaba da fuskantar karancin sabbin kudi a kasar nan, wani tsohon sanata ya ce ana takurawa 'yan Najeriya

Legas, Najeriya - Wata ‘yar Najeriya, Oluwadarasimi Omoseyin ta shiga hannun hukumar EFCC reshen jihar Legas bisa zargin cin zarafin kudi mai daraja na Naira, BBC Hausa ta ruwaito.

Hukumar ta EFCC ta kama matar ne bayan samun labarin ta yi amfani da sabbin Naira a wurin biki yayin da ake kokarin kawo sabbin ka’idojin takaita rike muraran kudi.

A cewar rahoto, matar ta kasance ‘yar fim kuma tana sana’ar gyaran fata, kuma ta shiga hannu ne bayan samun bayanan sirri a ranar Laraba 1 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Hukumar yan sanda ta yi magana game da mutumin da ya mutu a layi ciki banki

'Yar fim ta shiga tasku, ta EFCC ta kama ta bisa laifin lika kudi a gidan biki
'Yar Fim a Najeriya Ta Shiga Hannu Bayan Gano Ta Lika Sabbin Naira a Gidan Biki | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Idan baku manta ba, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kirkiri sabbin kudi tare da kaddamar dasu a kwanakin baya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kudaden sun hada da N200, N500 da N1000, kuma tsoffi za su daina amfani daga ranar 10 ga watan Fabrairu.

‘Yar Najeriya ta tattaka Naira a gidan biki

A baya an ga matashiyar mai shekaru 31 a cikin wani bidiyon da ya yadu a kafar yanar gizo, inda take lika sabbin Naira a wurin biki.

Hakazalika, bidiyon ya nuna lokacin da take cancarewa da rawa tana take kudaden ga kuma na’urar daudauka na daukar komai, PM News ta ruwaito.

Wannan lamari dai ya jawo cece-kuce a Najeriya, har ta kai wasu na dasa alamar tambayar cewa, shin ba talaka bane kadai ke shan wahalar samun sabbin kudin a Najeriya ba?

Kayayyakin da aka kama tare da ‘yar fim din

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Fusatattun Matasa Yan Zanga-Zanga Sun Kai Hari Ofishin Gwamna

A cewar rahoto, EFCC ta kama kayayyaki da dama a hannun matar; ciki har da mota kirar Range Rover, wayar iPhone da dai sauran kayayyakin alatu.

A halin da ake ciki, jami’an EFCC na ci gaba da bincike kan lamarin tare da tabbatar da an gurfanar da ita a gaban kuliya manta sabo.

Hukumar EFCC da ta ICPC sun sha alwashin kame dukkan wadanda ke wulakanta kudin kasar nan da kuma siyar dasu ba gaira babu dalili.

Har yanzu 'yan Najeriya na fara da karancin Naira, Shehu Sani ya caccaki CBN bisa kawo wannan doka ta takaita kudi a hannun jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel