An Sake Korar Ma'aikata da Yawa a Jihar Kaduna Kan Wasu Laifuka Daban-Daban

An Sake Korar Ma'aikata da Yawa a Jihar Kaduna Kan Wasu Laifuka Daban-Daban

  • Kanfanin wutar lantarki na Kaduna ya kori ma'aikatansa akalla 39 daga aiki bisa zargin aikata laifuka daban daban
  • A wata sanarwa da kakakin kamfanin, Abdulazeez Abdullahi, ya fitar ya bayyana wasu daga cikin laifun da suka ja aka sallame su
  • Ya ce kamfanin Kaduna Electric bai ji daɗin abin da suka aikata ba domin zai iya maida hannun agogo baya a a ci gaban da yake samu

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Kamfanin Wutar Lantarki na jihar Kaduna (Kaduna Electric) ya sanar da korar ma’aikatan da ba su gaza 39 ba bisa wasu laifuka da suka saba wa tsarin kamfanin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban sashin sadarwa da yaɗa labarai na kamfanin, Abdulazeez Abdullahi, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Likitoci sun yanke wa jarumin fina-finan Najeriya kafa don ceto ransa

Kamfanin wutar lantarki na Kaduna ya ƙori ma'aikata.
An Sake Korar Ma'aikata da Yawa a Jihar Kaduna Kan Wasu Laifuka Daban-Daban Hoto: punchng
Asali: UGC

Ya bayyana cewa laifukan da ma'aikatan suka aikata har aka kore su sun haɗa da karkatar kuɗaɗen kamfani, zamba, wuce gona da iri da kuma tserewa daga wurin aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi ya yi bayanin cewa waɗannan laifuka sun saɓa wa kundin sharuɗɗan ɗaukar aiki wanda aka yi wa garambawul kuma shugabannin kwadago suka aminta.

Da yiwuwar su funkanci shari'a

Sanarwar ta kara da cewa ayyukan laifin da ma’aikatan da aka kora suka aikata ya yi illa ga dukiyar kamfanin, don haka akwai bukatar a duba su da kuma yin nazari.

A cewar sanarwar,  kamfanin ya yi matukar fusata kan duk wasu ayyukan damfara da ma’aikatan ke yi kuma zai dauki matakin da ya dace ta hanyar hukunta duk wadanda aka kama.

Yayin da yake fatan korar da aka yi za ta zama izina ga saura, kamfanin ya shawarci abokan cinikin da su daina yin mu’amala da duk wani mai hada baki da ‘yan damfara.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da walkiya ta kashe dalibai suna tsaka da buga kwalla a Anambra

"Muna kira ga abokan cinikinmu da su gaggauta kai rahoton duk wani aikin zamba da suka ga an yi wa kwastomomin mu, " in ji sanarwan.

Yanzu na fara a siyasa - Obi

A wani rahoton kuma Mista Peter Obi ya ce tafiyar siyasar da ya ɗauko ta neman shugabancin Najeriya yanzu aka fara, ba zai haƙura haka nan ba.

Tsohon gwamnan ya nuna alamun cewa zai sake gwabza neman ɗarewa kujera lamba ɗaya a zaben shugaban ƙasa na 2027.

Asali: Legit.ng

Online view pixel