“Ku Yi Transfa”: Uwar Gayya Ta Taka Rawa Rike Da Lambar Akant Yayin Wani Biki, Bidiyon Ya Dauka Hankali

“Ku Yi Transfa”: Uwar Gayya Ta Taka Rawa Rike Da Lambar Akant Yayin Wani Biki, Bidiyon Ya Dauka Hankali

  • Wata matashiya yar Najeriya wacce ta halarci wani taron biki a daidai lokacin da ake fama da rashin tsabar kudi ta yanke shawarar taka rawa da lambar akant dinta
  • A wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, matashiyar ta rubuta lambar bankin nata a kan wata takarda sannan ta rike tana rawa da shi
  • Ana sa ran wadanda ba su je da tsabar kudi don yin liki a bikin ba za su tura mata kudin ta hanyar transfa

Wani bidiyo da aka wallafa a Instagram ya nuno wata matashiya yar Najeriya tana rawa rike da lambar akant rubuce a kan wata takarda.

Matashiyar ta kasance sanye da hadaddiyar doguwar riga irin na amare kalar ruwan hoda,

Mace na taka rawa
“Ku Yi Transfa”: Yar Najeriya Ta Taka Rawa Rike Da Lambar Akant Yayin Wani Biki, Bidiyon Ya Dauka Hankali Hoto: @pricelesshairs
Asali: Instagram

Da alama, ana sanya ran mutanen da suka halarci shagalin bikin da basu da tsabar kudin likawa saboda karancin takardun naira za su aika nasu gudunmawar ta hanyar yin transfa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwa Tana Murna Bayan Saurayinta Ya Kai ta SIyan Gwanjo Kafin Zuwa Ranar Masoya ta Duniya

A cikin bidiyon, an gano matashiyar rike da wata yar takarda a hannunta yayin da take rawa ita kadai. Ta rike abarta kamar mafici irin na zamani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai idan mutum ya kura ido, zai ga cewa abun da take nuna wa ba komai bane face lambar akant.

Karara ta fito fili ta bayyana cewa so take mutanen da basu zo da tsabar kudi ba su yi mata transfa.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da yan Najeriya ke matukar shan wahala wajen samun tsabar kudi saboda manufar CBN na komawa ga yin harkoki ta yanar gizo.

Jama'a sun yi martani

@og.tega ta tambaya:

"Har yanzu kina daukar Zenith kan ki tsaye? Ba ki ga komai ba."

@ewatomisin199 ya tambaya:

"Yaya ake ciki menene sabon labari game da batun takardun Naira."

Kara karanta wannan

Mace Mai Juna Biyu Ta Mutu Saboda Asibiti Sun Ce Sai 'Cash' a Kaduna

@coker_slake ta yi martani:

"Ina mai ba da hakuri na zo latti. Na je taya CBN hada fentin yau ne."

@zinny_cleo ta ce:

"Tsarin ya yi kyau amma bankin ne ya bata shi."

Yadda wani tsoho ya sharbi kuka a cikin baki saboda ya gaza cire kudinsa, ya tsinewa CBN

A wani labarin kuma, wani tsohon mutum ya taba zukata jama'a duba da yadda ya dunga sharbar kuka a cikin banki saboda ya gaza samun kudinsa a hannu.

Dattijon ya ce tsawon kwanaki yana yawo da yunwa ga shi yana bukatar siyan magani amma babu hali saboda tsarin CBN ya hana masa cire kudinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng