Bidiyoyin: Yadda Matasa Suka Yi Ruwan Liki Harda Su Daloli A Wajen Shagalin Dinan Dan Sarkin Kano

Bidiyoyin: Yadda Matasa Suka Yi Ruwan Liki Harda Su Daloli A Wajen Shagalin Dinan Dan Sarkin Kano

  • An yi shagalin dina a bikin Kabiru Aminu Bayero, dan sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, da kyakkyawar amaryarsa Aisha Ummaran Kwabo
  • Matasa sun yi ruwan kudi a wajen wannan shagali inda aka lika bandir-bandir na kudi ciki harda su daloli
  • Tuni bidiyoyin wannan shagali ya yadu a shafukan soshiyal midiya inda jama'a suka tofa albarkacin bakunansu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A ranar Juma’a, 26 ga watan Agusta ne dubban jama’a suka shaida daurin aure tsakanin Kabiru Aminu Bayero, dan sarkin Kano Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, da kyakkyawar amaryarsa Aisha Ummaran Kwabo.

Duk a cikin shagalin bikin, an gudanar da wani kasaitaccen liyafar Dina wanda ya samu halartan amarya da ango.

Matasa na liki
Bidiyoyin: Yadda Matasa Suka Yi Ruwan Liki Harda Su Daloli A Wajen Shagalin Dinan Dan Sarkin Kano Hoto: fashionseriesng
Asali: Instagram

Kamar yadda aka saba, yan uwa da abokan sabbin ma'auratan sun yi masu kara wajen kasancewa a taron.

Kara karanta wannan

Bidiyon Shigowar Kasaita da Iyalan Bayero Suka yi Wurin Liyafar Auren Kabiru Aminu Bayero

An kuma yi ruwan kudi inda matasa suka sha likin kudade bandir-bandir ciki harda masu ruwan daloli.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bidiyoyin da shafin fashionseriesng ya wallafa a Instagram, an gano angon da amaryarsa Aisha zaune kan kujeru da aka tanadar masu yayin da abokansa suka mamaye su suna masu yayyafin kudi a ka.

Kalli bidiyoyin a kasa:

Jama’a sun yi martani

hassay10 ta yi martani:

“Basune suke Neman kudinba shiyasa,basusan ciwon kudinba,,,Dan Haka duk yadda sukayi da kudin daidaine, duk Wanda yasan zafin nema baya Almubazzaranci da kudi.”

exclusiv_boutique_ ta ce:

“Allah sarki kudin kasar mu.”

khadis_cuisine ta ce:

“Allah sarki Asuu.”

Bidiyon Yadda Amarya Ta cafke Dalolin Da Aka Lika Mata A Wajen Liyafar Bikinta

A wani labari na daban, mun ji cewa bisa al’ada idan aka ce ana taro imma na aure ko suna a kan tanadi tawaga na musamman wadanda aikinsu a wannan wuri shine kwashe kudaden liki.

Kara karanta wannan

Bidiyoyin Shagalin Dinan Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi

Sai dai kuma wata amarya ta shayar da mutane mamaki bayan da aka gano ta a cikin bidiyo tana cafke kudaden da ake lika mata.

A cikin bidiyon wanda ya yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano amaryar wacce aka ambata da suna Aisha a filin rawa yayinda wata hajiya ta bude jakar hannunta ya zaro daloli tana lika amaryar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel