“Ina Samu a Wajen Wata Matar”: Magidanci Ya Koka Yayin da Matarsa Ke Hana Shi Hakkinsa Na Aure

“Ina Samu a Wajen Wata Matar”: Magidanci Ya Koka Yayin da Matarsa Ke Hana Shi Hakkinsa Na Aure

  • Wani matashi dan Najeriya ya koka cewa matarsa ta dauki tsawon lokaci tana hana shi hakkinsa na auratayya
  • Ya ce matarsa na yawan korafin jin kasala da gajiya amma ya bayyana cewa shi ya gajin da jin uzurinta
  • Domin kashe kishirwansa, mutumin ya ce ya samu wata mata da ke ba shi damar yin sharholiya da ita a duk lokacin da yake so

Wani mutum ya ce a yanzu yana tarawa da wata mata a wajen gidansa na sunnah a duk lokacin da matarsa ta hana shi hakkinsa na auratayya.

A wani labari da ya yadu a Twitter, mutumin ya ce matarsa na yawan korafi, tana mai ba shi dalilai da suka sa ba za su iya raya sunnah ba.

Miji ya koka yayin da mata ke hana shi hakkinsa
An yi amfani da hoton don misali ne kawai, mutanen ciki basu da alaka da labarin Hoto: Getty Images/Kateryna Onyshchuk and Vladimir Vladimirov.
Asali: Getty Images

Ya ce matarsa ta yi haihuwar karshe shekaru uku da suka wuce, amma ta ce lallai ba za su tara ba idan har ba a yi dabarun hana daukar ciki ba.

Kara karanta wannan

Mai wankin mota ya taro rigima, ya kwankwatsa motar kwastoma a garin dani

Wani mataki mijin ya dauka?

Kamar yadda ya bayyana, matar tasa ta ce lallai bata so ta dauki juna biyu, amma kuma ta ki yarda su yi tsarin iyali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sau daya yake ganin matarsa cikin makonni biyu saboda yana zama da aiki a Lagas ne. Domin gamsar da kansa, mutumin ya bayyana cewa yanzu yana da wata mata da yake tarawa da ita a Lagas.

“Yanzu bana nemanta kuma tun da ina da wacce ke kula da ni a inda nake.”

Mutumin da ya boye sunansa ya aika wani sako zuwa shafin @wizarab, inda shi kuma ya yada a Twitter.

Duba cikakken labarin a kasa:

Jama'a sun yi martani kan matar da ke hana mijinta hakkinsa

@TheRoyalHerbs ta ce:

"Gwanda ka je ka nemi wata matar sannan ka fara sabuwar rayuwa a inda kake saboda akwai abun da take boye maka."

Kara karanta wannan

Wani Mutum Ya Yi Ikirarin Soya Kaza Da Ruwa, Ya Saki Bidiyon Tsarin Da Ya bi

@ogunmusi ya ce:

"Magana ta gaskiya. Kafin auren tana kwana da shi kodayaushe. Bayan auren ya zame mata aiki."

@unknownthedj_ ta ce:

"Idan har ku dukka hudun kuna farin ciki. Su waye mu da za mu yi korafi?"

Legit Hausa ta tuntubi wata mai sharhi kan abubuwan da suka shafi zamantakewar ma’aurata don jin ta bakinta kan halin da wannan magidanci ya tsinci kansa.

Malama Amina Muhammad ta ce:

“Gaskiya yawancin lokuta matan aure su ke jefa mazajensu cikin halin bin matayen banza. A matsayinki na matar aure, wani uzuri kike da shi da zai hana ki yarda da mijin ki idan ya neme ki? A wannan zamani da ake ciki.
“A matsayinki na mace ke ya kamata ki tunkari mijinki na sunnah tun ma kafin ya neme ki domin tabbatar da ganin kin gamsar da shi a shimfida ta yadda ba zai ma ji sha’awar wata mace da ba halaliyarsa ba a waje.

Kara karanta wannan

Ana Min Kallon Ba Zan Iya Ba Saboda Na Iya Rawa, Gwamnan PDP

“Idan ma wata lalura ce da ke sai ki nemi magani, amma da zaran kin fara kauracewa mijinki a shimfida, ke ma kin san me kike kokarin jefa kanki a ciki.”

Dattijo ya sheke matarsa saboda kwanciyar aure

A wani labarin, wani dattijo mai shekaru 84 mai suna Gabriel Uhuwa, ya bayyana cewa shi ne ya kashe matarsa mai kimanin shekaru 75 a duniya.

Ya bayyana cewa ba ta yadda ta kwanta da shi, kuma labari ya iske shi cewa tana kwanciya da wasu Fastoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel