Mai Wankin Mota Ya Taro Rigima, Ya Kwankwatsa Motar Kwastoma a Garin Dani

Mai Wankin Mota Ya Taro Rigima, Ya Kwankwatsa Motar Kwastoma a Garin Dani

  • Wani mai sana'ar wankin mota ya jawowa kansa matsala yayin da ya wanke wata mota a wani yankin jihar Ribas
  • An ruwaito cewa, hakan ya faru ne bayan da ya wanke mota sai kawai ya yanke ya yi dani don gwada kwarewarsa
  • Ya zuwa yanzu, an ceto shi yayin da motar ta kwarzane shi kuwa ya tsallake mutuwa dakyar bayan an taimake shi

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar Ribas - Hotuna sun nuna yadda wani mai sana'ar wankin mota ya tsallake rijiya da baya yayin da aka ba shi mota ya wanke kawai ya hau don ya dana.

Wannan lamari dai ya faru ne a yankin Rumueme da ke Fatakwal a jihar Ribas, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Fubara ya gana da Wike, Ya ce ‘mai gida na har gobe’

Hatsarin mota.
Mai wankin mota ya yi hatsari da motar kwastoma yayin dani. Hoto: Justice Ori
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mai amfani da kafar Faccebook, Justice Ori ne ya yada wannan labarin da kuma hotunan yadda lamarin ya auku.

Daga dani an jawo babbar asara

A hotunan, an ga lokacin da motar ta gindaya a cikin kwalbati, kamarin da ya jawo hankalin jama'a da dama.

Yayin da yake yada hotunan, ya ce:
“Wannan ya faru ne da yammacin yau a unguwar Rumueme da ke Fatakwal, wani mutum ne ya tuko motarsa zuwa wajen wanki, mai wankin bayan ya wanke ta ya dauka don zuwa dani, sai kawai muka gan shi da motar a cikin kwalbati.
"Mutane da yawa ne suka hadu don taimaka masa ya fito a motar da kuma ceto ransa. Motar ta koke shi kuma mai ita bai ma san abin da ya faru ba har yanzu."

Wani ma ya aikata hakan

Kara karanta wannan

Kano: Kotun musulunci ta umurci magidanci ya karbi ɗan da ya ke kokwanton ba nasa bane

A wani labari mai kama da wannan, an yi cece-kuce yayin da wani mai wanki shi ma ya tuka motar da aka ba shi wanki, har ta kai ya bata ta kaca-kaca.

A ruwayar da muka samu, an ga bidiyon rikicin da ya barke a kafar TikTok, inda ake cece-kuce ko za a iya yafe masa aikata wannan mummunan asara ta ganganci.

Ana yawan samun lokuta da dama da masu wanki ke daukar abin hawan da aka ba shi su wanke, har ma a samu matsalar da ba a yi fata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel