"Har Yanzu Ban Yi Kwanciyar Aure Ba Da Matata Shekara Uku Bayan Aure": Magidanci Ya Koka

"Har Yanzu Ban Yi Kwanciyar Aure Ba Da Matata Shekara Uku Bayan Aure": Magidanci Ya Koka

  • Wani matashi ɗan Najeriya ya kasa samun damar yin kwanciyar aure da matarsa duk da sun shekara uku da yin aure
  • An tattaro cewa matashin ya jaraba hanyoyi da domin ganin hakan ta faru amma lamarin ya ci tura inda haƙarsa bata cimma ruwa ba
  • Wani mai amfani da manhajar Twitter wanda ya sanya labarin ya bayyana cewa lamarin ya kai wani lokaci har kira abokansa ya yi su ɗaure mai ita

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Labarin wani matashi ɗan Najeriya wanda ya kasa samun damar sanin cewa ya yi aure ya sosa zukatan mutane da dama.

A tsawon shekara uku da suka kwashe tare da matarsa, ta ƙi yarda su yi kwanciyar aure tun bayan da aka ɗaura musu igiyar aure.

Matashi ya koka bayan matarsa ta ki yarda su yi kwanciyar aure
Shekara uku da aure amma babu abinda ya shiga tsakaninsu Hoto: Goodboy Picture Company/ Getty Images.
Asali: Getty Images

Ko da aka so jin dalilin da ya sanya ta ƙi yarda su raya Sunnah da mijin nata, matar ta bayyana cewa ita kaɗai ta san dalilin da ya sanya ta ƙi yarda su yi hakan.

Kara karanta wannan

"Ya Daina Nuna Mun Soyayya" Wata Mata Ta Roki Kotu Ta Raba Auren Kuma Ta Umarci Mijin Ya Riƙa Biyanta N30,000

Mijin wanda ya fusata har gayyato abokansa ya yi domin su ɗaure masa ita ya yi amfani da ita, amma daga baya ya sauya shawara inda ya kwanceta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Al_Shekarau ya rubuta a Twitter cewa:

"Wani abokinmu ya yi aure shekara uku da suka wuce amma har yau bai taɓa kwanciyar aure da matarsa ba. Ta hana shi ya yi amfani da ita saboda wasu dalilai na ƙashin kanta sannan har yanzu bai saketa ba."
"Akwai wani lokaci da wasu daga cikin abokanmu suka ɗaure masa ita akan gado amma sai ya kwanceta suna barin wajen. Wallahi labarin ya auku da gaske."

Masu amfani da yanar gizo sun yi martani bayan matar aure ta bari su raya Sunnah da mijinta

Ridbay ya rubuta: "

"Wasu daga cikin abokan ku sun ɗaure masa ita akan gado? Bayan ita ba ragon layya bace. Ya yi abinda ya dace da ya kwanceta."

Kara karanta wannan

“Da Ka Sa N200”: Dan Najeriya Ya Buga Caca Da N10, Ya Lashe Miliyan N2, Mutane Sun Yi Cece-kuce

mkaeey ya rubuta:

"Tana da aljanu gaskiya."

Asiya Rodrigo ta rubuta:

"Ta iya yiwuwa ya san dalilin amma abokansa basu sani ba. Yakamata su bar shiga abinda babu ruwansu a ciki ta hanyar ƙin taɓa mace, matar aure ko mara aure ba tare da sahalewarta ba."

Faee! ta rubuta:

"Tab ta yi haƙuri domin da ni ce suna kwance ni sai ofishin ƴan sanda."

Bello Shehu Maude ya rubuta:

"Jan Kati bai da amfani ne? Iyayenta ya kamata su fara jin wannan kafin ta kai ga Yellow Card ballantana Red Card"

Magidanci Ya Nemi Kotu Ta Datse Igiyar Aurensa Da Matarsa

A wani labarin kuma, wani magidanci ya garzaya kotu neman ta datse igiyar aurensa da matarsa wacce suka shekara 22 tare da aure a tsakaninsu.

Magidancin dai ya maka matar tasa a gaban kotun ne saboda a cewarsa bata ganin darajarsa da ta iyayensa, kuma har duka saurayinta yake laƙada masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel