Yar Shekaru 80 Ta Ce Har Yanzu Ita Tsarkakkiya Ce, Bata Taba Kwanciya Da Namiji Ba

Yar Shekaru 80 Ta Ce Har Yanzu Ita Tsarkakkiya Ce, Bata Taba Kwanciya Da Namiji Ba

  • Annostacia Mukarukaka ta yi ikirarin cewa har yanzu ita tsarkakkiya ce duk da cewar ta taba aure a rayuwarta
  • Rayuwar Mukarukaka cike yake da tashin hankali tun daga kuruciya zuwa ga cin zarafi da rayuwar kadaici, rayuwa da ke tattare da kunci
  • Rayuwar kadaici da tsohuwar ta yi saboda rashin kwanciyar hankali, rashin lafiya da sauransu ya nuna juriyarta game da kalubalen rayuwa da kokarinta na rike kanta

Rwanda - Wata dattijuwar mata mai suna, Annostacia Mukarukaka, ta yi ikirarin cewa har yanzu ita tsarkakkiya ce a shekaru 80 duk da cewar ta taba auren wani namiji na dan lokaci.

Mukarukaka bata taba sanin da namiji ba
Yar Shekaru 80 Ta Ce Har Yanzu Ita Tsarkakkiya Ce, Bata Taba Kwanci Da Namiji Ba Hoto: Afrimax English.
Asali: Youtube

Mukarukakata rasa iyayenta biyu

"Na auri wani mutum, amma yana kwanciya da sauran mata. Ban san komai game da kwanciyar aure ba har sai da kawayena suka fara magana a kansa lokacin da na tambaye shi dalilin da yasa bamu yi kwanciyar aure ba tare, amma sai ya yi watsi da ni sannan ya yi tafiyarsa," ta sanar da Afrimax English.

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

Mukarukaka bata ji dadin kuruciyarta ba ma, domin mahaifiyarta ta rasu lokacin da take da shekaru hudu a duniya, insa ta barta a hannun kakarta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dan takaitaccen rayuwa a DRC

Kakar tata ma ta mutu bayan dan gajeren lokaci, sannan aka bar karamar yarinyar a hannun wata muguwar kishiyar uwa. Lokacin da tsarin ya ki aiki, sai ta tafi Damokradiyyar Congo domin ci gaba da rayuwa.

"Ana ba ni magani don kada ni din fatalwa ce. Na sake komawa rayuwa da kishiyar uwata, amma sai ta fara muzguna mun. Mukarukaka", ta yi bayani.

Mutuwar mahaifinta ya kara tabarbarar da lamura a rayuwarta, kuma haka ta kare da auren mutumin da bai dace ba. Ba ta da 'ya'ya, abokai, ko dangi, don haka ta koyi yin rayuwa a haka.

Me yasa Mukarukaka ke da kumburarrun idanu?

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: An Fadawa Tinubu Abu Daya Tak Da Zai Yi Don Shawo Kan Matsalar Tsaro A Jihar Arewa, Ta Nemi Bukata

"Ya ci gaba da tarawa da sauran mata da daukar kayayyaki," inji ta.
"Na yi kokarin yin abubuwa don samun kudin siyan abinci, amma kamar yadda kuka gani, ba abu ne mai sauki ba ko kadan. Wasu lokutan da wuya na iya tashi daga gado," ta yi bayani.

Idan Mukarukaka ta ji kadaici, tana kallon hotunan wasu mtane da aka yanyanka daga cikin musalla kamar da sune ta yi rayuwa.

Tsohuwar na bacci a kan gado mara fasali, sannan abuncin da take dafawa guda daya ne kullun. Tana rayuwa a wani tsohon gida kuma ana fargabar zai iya rushewa a kowani lokaci.

Mukarukaka na kuma fama da wasu ciwuka a kanta, kuma ta ce ta na zargin cewa suna sa idanunta kumbura a kowace safiya.

Bata bani hakkina: Matashi ya koka watanni 3 bayan aurensa

A wani labari na daban, mun ji cewa watanni uku bayan daura aurensu da budurwa yar shekaru 17, matashin ya je shafin soshiyal midiya don nuna rashin jin dadinsa game da yadda zamansu ke gudana a gidan aurensu.

A cikin wani bidiyo da ya wallafa a TikTok, matashin mai shekaru 20 ya koaka cewa bait aba sanin matar tasa ‘ya mace ba tun bayan da suka yi aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel