Ku Dena Yi Wa Mazajenku Rowa Yayin Kwanciyar Aure, Likita Ya Faɗa Wa Mata Illar Yin Hakan

Ku Dena Yi Wa Mazajenku Rowa Yayin Kwanciyar Aure, Likita Ya Faɗa Wa Mata Illar Yin Hakan

  • Wani kwararren likitan mata, Eric Okunna ya shawarci matan aure su dena hana mazajensu hakkin kwanciyar aure
  • Dr Okunna ya ce kwanciyar aure da na matukar alfano da ya hada da kwantar da hankali, yaye damuwa da motsa jiki da inganta garkuwar jiki
  • Likitan ya yi gargadin cewa ma'aurata su dena hana junansu hakkin kwanciyar aure a lokacin da suka samu sabani don hakan na iya yin sanadin rabuwa

Jihar Anambra - Eric Okunna, wani kwararren likitan mata, ya ce alfano da ke tattare da kwanciyar aure mai nagarta ba zai misaltu ba, rahon The Cable.

A cewar kamfanin dillancin labarai, NAN, likitan ya tambayi ra'ayoyin wasu mazauna Awka, Jihar Anambra, kan batutuwan da suka shafi rayuwar aure musamman kwanciyar aure.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Kirkiro Sabuwar Hanyar Tatsar Kudi Daga Masu Hawa Titi

Namiji da Mace.
Kwararren Likita Ya Shawarci Mata Su Dena Hana Maza Hakkin Kwanciyar Aure, Ya Fadi Illolin Hakan. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

Ya ce wadanda suka amsa tambayoyinsa sun ce bai dace ma'aurata su rika hana juna hakkin kwanciyar aure ba musamman mata ga mijinta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Okunna ya ce wasu sun ce namiji ne shugaba a gidansa don haka bai dace a rika masa wasa da 'hankali' ba.

Ya ce ingantacciyar kwanciyar aure na karfafa soyayya tsakanin ma'aurata.

Ya kuma ce yawan neman kwanciyar aure daga bangaren na miji 'ka iya jefa mata cikin wani yanayi' hakan kuma ya janyo wa namijin cutuwa.

Okunna ya ce yana da muhimmanci a rika daukar aure a matsayin abu mai muhimmanci, don haka, kada mata su rika azabtar da mazansu ta hanyar hana su kwanciya da su.

Kwararren likitan ya kara da cewa bai kamata a rika amfani da kwanciyar aure a matsayin abin ramuwar gayya ba idan an samu matsala tsakanin mata da miji.

Kara karanta wannan

Sallah: Tsadar Raguna Ba Zai Hana Mu More Bikin Sallah Ba, 'Yan Najeriya Sun Magantu

Fa'idar kwanciyar aure a tsakanin mata da miji, in ji likita

"Kwanciyar aure kansa magani ne da ke kwantar da hankali da kallubalen rayuwa kamar damuwa, shauki kuma motsa jiki ne da ke inganta lafiya," in ji Okunna.
"Rashin jituwa tsakanin masoya ba sabon abu bane har da ma'aurata. Ba dai-dai bane ma'aurata su rika hana juna kwanciyar auren idan sun samu rashin jituwa."
"A maimakon hakan, a rika amfani da kwanciyar aure don warware matsala tsakanin mata da miji saboda yana iya kwantar da hankula a maimakon abin raba kai.
"Kauracewa kwanciya da juna a aure ba hanya bace mai kyau na warware matsaloli a aure kuma kan iya sanadin mutuwar aure."

A cewar likitan, a rika yin kwanciyar auren dai-dai gwargwado ta yadda ma'auratan za su gamsu su yi maganin kadaici.

Kotu ta raba auren shekara 18 saboda mata ba ta gamsar da mijinta

A wani rahotonn, wata kotu da ke Mapo, Ibadan a ranar Juma'a ta raba auren shekara 18 tsakanin wani malami, Juel Olutunji da matarsa saboda rashin gamsuwa wurin kwanciyar aure.

Kara karanta wannan

Ba Ka da Tausayi: Peter Obi Ya Tsoma Baki a Rusau Din Kanawa, Ya Yi Wa Abba Gida Gida Kaca-Kaca

Da ya yanke hukunci, Cif Ademola Odunade ya ce an raba auren saboda samun zaman lafiya tsakanin Olutunji da Blessing kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya bawa Olutunji ikon rike yaransu biyu na farko ita kuma Blessing ya bar mata sauran yaron ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel