'Yan Bindiga Sun Sake Kai Harin Ta'addanci a Jihar Sokoto, Sun Kashe Rayuka

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Harin Ta'addanci a Jihar Sokoto, Sun Kashe Rayuka

  • Wasu 'yan sa'kai sun fusata sun kai harin ɗaukar fansa rugar Fulani jim kaɗan bayan wasu mahara sun kashe jama'a a kauyen Soro
  • Rahoto ya nuna yan bindigan da ake zargin Fulani ne sun kashe mutane uku kana suka yi awon gaba da wasu da dama a jihar Sakkwato
  • Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa tuni kwamishina ya shiga tsakani kuma a yanzu an kwantar da hankalin ƙauyukan guda biyu

Sokoto - 'Yan banga sun kai harin ɗaukar fansa kan Rugogin Fulani bayan wasu 'yan fashin daji sun kai sabon hari kan fararen hula a jihar Sakkwato.

Jaridar Daily Trust ta ce yan banga sun kai farmaki kauyukan Fulani ne bayan mahara sun kashe mutum 3, sun sace wasu da dama a kauyen Soro, ƙaramar hukumar Binji da ke jihar.

Kara karanta wannan

‘Yan Boko Haram Sun Yi Kashe-Kashe, Sun Dauke Wasu Sarakuna 2 a jihar Borno

Harin yan bindiga a jihar Sakkwato.
'Yan Bindiga Sun Sake Kai Harin Ta'addanci a Jihar Sokoto, Sun Kashe Rayuka Hoto: channelstv
Asali: Twitter

A cewar wasu majiyoyi daga ƙauyen, 'yan bindigan dajin sun shiga ƙauyen Soro ne da misalin ƙarfe 1:00 na tsakar daren ranar Litinin da ta wuce.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya bayanansa ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sun shiga da mayaƙa masu ɗumbin yawa tare da wasu dabbobi da muke tsamanin sun yi ƙwacensu ne a wasu ƙauyukan da ke kusa."
"Sun kashe mana mutum uku kuma sun jikkata wasu uku, sannan sun yi awon gaba da wasu ciki harda 'yan gida ɗaya."
"Jim kaɗan bayan haka 'Yan sa'kai suka haɗa dakaru suka kai farmaki rugar fulani da ke kusa, suka halaka musu mutane kana suka ƙona gidaje."

Mutumin ya ƙara da cewa:

"An yi ta rade-radin cewa Fulanin sun yi taro sa'o'i kadan kafin harin. Don haka, mutanenmu suka yi zargin cewa daga nan aka kitsa harin saboda akwai tsama taskanin ƙauyukan biyu."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Ɗana Tarko, Sun Yi Garkuwa da Babban Jami'in Sojojin Najeriya

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

“Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ’yan fashin daji ne sun kai farmaki kan al’ummar garin Soro amma dakarun mu tare da goyon bayan jami’an soji sun dakile harin."
“Amma ‘yan bindigan saboda takaici suka kona wasu gidaje, sakamakon haka uku daga cikin mazauna garin suka rasa rayukansu yayin da wasu kadan suka samu raunuka daban-daban."
“An kai harin ramuwar gayya amma mutanenmu sun sami damar shawo kan lamarin bayan kwamishinan ‘yan sanda, Ali Kaigama ya zauna da shugabannin ƙauyukan biyu."

Jirgin Ruwa Dauke da Fasinjoji 22 Ya Gamu da Hatsari a Jihar Neja

A wani rahoton kuma Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja NSEMA ta tabbatar da cewa wani jirgin ruwa ya kife da mutane sama da 20 ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan Bindigan da Suka Yi Garkuwa da Kwamishina a Jihar APC Sun Aiko da Saƙo Mai Ɗaga Hankali

A cewar hukumar, Jirgin ya taso ne daga ƙauyen Ƙasabu zuwa garin Yauri, a hanya ya nutse da fasinjoji da tsakar rana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel