Jirgin Ruwa Dauke da Fasinjoji 22 Ya Gamu da Hatsari a Jihar Neja

Jirgin Ruwa Dauke da Fasinjoji 22 Ya Gamu da Hatsari a Jihar Neja

  • Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja NSEMA ta tabbatar da cewa wani jirgin ruwa ya kife da mutane sama da 20 ranar Litinin
  • A cewar hukumar, Jirgin ya taso ne daga ƙauyen Ƙasabu zuwa garin Yauri, a hanya ya nutse da fasinjoji da tsakar rana
  • Shugaban hukumar ya ce har yanzun ba a ceto ko mutum ɗaya ba saboda sai daga baya aka sanar da faruwar lamarin

Jihar Neja - Wani jirgin ruwa da ya dauko akalla fasinjoji 22 daga kauyen Kasabu, ƙaramar hukumar Agwara ta jihar Neja zuwa garin Yauri, ya gamu da haɗari.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja, Salisu Garba ne ya bayyana haka ga hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a Minna, babban birnin jihar ranar Litinin.

Jirgin ruwa ya kife da mutane a jihar Neja.
Jirgin Ruwa Dauke da Fasinjoji 22 Ya Gamu da Hatsari a Jihar Neja Hoto: punchng
Asali: UGC

Ya ce hukumar ta samu rahoton kifewar jirgin ruwan wanda ya kife da misalin karfe 11 zuwa 12 na tsakar rana jiya Litinin, kamar yadda jaridar Punch ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Yi Kalamai Masu Ratsa Zuciya Bayan Kotu Ta Tabbatar Da Nasararsa a Zabe

A cewarsa, wani fasinja da aka tsamo da ransa ya faɗa wa hukumar bada agajim cewa Kwale-Kwale ya ɗebo kusan mutum 22 sa'ilin da ya kife a cikin ruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Garba ya bayyana cewa a halin yanzun mutanen yankin da suka iya ruwa da masu Kwale-Kwalen na kan aikin ceto fasinjojin da suka nutse bisa kulawar jami'in hukumar mai kula da Agwara.

Wane hali ake ciki a ƙoƙarin ceto mutanen?

Salisu Garba ya ƙara da bayanin cewa har yanzu ba a kai ga samun nasarar tsamo ko mutum ɗaya ba, inda ya ƙara da cewa haɗarin ya auku ne a ranar da ake cin kasuwar Yauri.

Shugaban hukumar NSEMA ya ƙara da cewa sai bayan kasuwa ta watse ne sannan iyalan fasinjojin suka sanar da cewa 'yan uwansu sun ɓata.

A 'yan watannin nan ana yawan samun hatsarin jirgin ruwa a jihar Neja da wasu jihohin arewacin Najeriya, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dama, Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

An Samu Asarar Rai Bayan Rufin Wani Gini Ya Rufto a Jihar Taraba

Gwamna Abdullahi Sule Dam Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotun Zabe

A wani rahoton na daban kuma Gwamna Sule na jihar Nasarawa ya ce zai daukaka hukuncin da Kotun zabe ta yanke zuwa gaba domin kwato hakkinsa.

Ya ce hukuncin wanda ya soke nasarar da ya samu, koma baya ne da zai dauki darasi daga ciki kana ya shirya fitowa da karfi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel