Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Tsoshon Janar Na Sojojin Najeriya a Jihar Imo

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Tsoshon Janar Na Sojojin Najeriya a Jihar Imo

  • Miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da Manjo janar na rundunar sojin Najeriya wanda ya yi ritaya daga aiki a jihar Imo
  • Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaro sun baza komarsu domin kuɓutar da shi kuma ga dukkan alamu suna hanyar samun nasara
  • A tattaro cewa maharan sun yi awon gaba da mutumin ne yayin da yake kan hanyar zuwa wani wuri, sun haɗa da motarsa

Jihar Imo - Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani tsohon soja, Manjo Janar mai ritaya Richard Duru, a karamar hukumar Owerri ta Arewa da ke jihar Imo.

Jaridar Punch ta tattaro cewa 'yan bindigan sun samu nasarar yin garkuwa da Mista Duru ne yayin da suka kai masa harin kwantan ɓauna a jihar ta Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

'Yan Bindigan da Suka Yi Garkuwa da Kwamishina a Jihar APC Sun Aiko da Saƙo Mai Ɗaga Hankali

An sace tsohon babban soja a jihar Imo.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Tsoshon Janar Na Sojojin Najeriya a Jihar Imo Hoto: punchng
Asali: UGC

Yayin da aka tuntuɓi Daraktan hulɗa da jama'a na rundunar sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, ba a same shi ba domin kiran wayar aka masa baya shiga.

Amma wasu majiyoyi biyu a rundunar soji, wadanda suka tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a, sun bayyana cewa an tura sojoji domin su ceto shi cikin ƙoshin lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce:

“Lamarin ba sabo bane. An sace shi a makon da ya gabata ko wani abu mai kama da haka. Maharan sun tafi da motarsa yayin da suka faramake shi a kan hanya."
"Ana kan ƙoƙarin kubutar da shi, jami'an tsaro na samun ci gaba, suna dab da gano 'yan ta'addan. Ina baku tabbacin cewa sojojin mu da haɗin guiwar sauran jami'an tsaro zasu kuɓutar da shi."

A cewar wasu bayanai da Sahara Reporters ta tattara kan lamarin, dakarun soji sun bi diddigin lambar tsohon babban jami'in sojan zuwa Mbaitoli a jihar Kafin a kashe wayar.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Harbi Dalibai 3, Sun Sace Wata a Kwalejin Kimiyya a Wata Jihar Arewa

"Mun bi diddigi lambar wayansa har zuwa Mbaitoli a jihar Imo gabanin daga bisani a kashe wayar gaba ɗaya, muna kan aikin lalubo inda maharan suka buya, mu ceto tsohon janar ɗin."

Benue: Masu Garkuwa da Kwamishina Sun Nemi Kudin Fansa N60m

A wani rahoton na daban Masu garkuwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Benuwai sun turo saƙo mai ɗaga hankali ta wayar ɗaya daga cikin iyalansa.

'Yan bindigan sun nemi a lalubo musu kuɗi Naira miliyan 60 a matsayin kuɗin fansa kafin su sako Mista Mathew Abo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel