Auren zawarawa: Ganduje ya biya miliyan N30 a matsayin kudin sadakin amare 1500

Auren zawarawa: Ganduje ya biya miliyan N30 a matsayin kudin sadakin amare 1500

A ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu, ne gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya biya miliyan N30 a matsayin kudin sadakin zawarawa 1500 da suka fito daga kananan hukumomi 44 da gwamnatin jihar Kano ta aurar da su.

Da yake sanar da hakan a cikin jawabin da sakataren sa na yada labarai, Abba Anwar, ya sanya wa hannu, Ganduje ya ce za a yi amfani da wani bangare na kudin da gwamnatin ta bayar domin saya wa sabbin amaren kayan daki da suka hada da katifa, gado, madubi da sauran su.

Gwamnatin ta ce ta ware N200,000 a matsayin kudin sadaki ga kowacce amarya daga cikin zawarawan 1500.

"Ba iya kudin sadaki gwamnati ta biya wa amaren ba, a cikin aiyukan alheri da wannan gwamnati ta saba yi' za ta saya wa kowacce amarya kayan daki da suka hada da gado, madub, katifu da sauran su.

Auren zawarawa: Ganduje ya biya miliyan N30 a matsayin kudin sadakin amare 1500
Auren zawarawa
Asali: Twitter

"Har labule da ledar tsakar daki da saitin kujeru da suka hada da masu daukan mutum uku da kananu, gwamnati za ta saya wa ma'auratan.

DUBA WANNAN: Shugabancin majalisu: Mambobi da shugabannin PDP sun zabi 'yan takarar da zasu goya wa baya

"Za mu dinka wa kowanne ango sabuwar shadda da zai saka domin ya fito fes cikin farinciki kamar yadda kowanne ango ke kasancewa ranar daurin auren sa," a cewar jawabin.

Anwar ya kara da cewa gwamnatin tayi haka ne domin saukaka wa ma'auratan wahalhalu da kashe kudi da sabon aure ke zuwa da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel