Auren Zaurawa: Mata Sun Ƙyalla, Sun Hango ‘Yan Majalisa da Jagororin Kwankwasiyya

Auren Zaurawa: Mata Sun Ƙyalla, Sun Hango ‘Yan Majalisa da Jagororin Kwankwasiyya

  • ‘Yan kungiyar matan Kwankwasiyya sun yi maraba da auren zaurawa da gwamnatin Kano za tayi
  • Shafa’atu Ahmad ta shaida cewa daga cikinsu akwai masu harin ‘yan Siyasar da suka yi wa aiki a NNPP
  • Har shi kan shi shugaban Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa bai tsira daga burin matan na Kano ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Wasu daga cikin jagororin matan Kwankwasiyya, sun yi magana a kan shirin auren zaurawa da gwamnatin jihar Kano ta dawo da shi.

Da ‘yan jarida su ka yi hira da Shafa’atu Ahmad a gidan rediyon Freedom, ta shaida cewa matan da za a aurar sun hango mazan da suke so.

Shafa’atu Ahmad ta na cikin ‘yar kungiyar matan Kwankwasiyya da su ka bada gudumuwa a zabe, a dalilin haka wasu su ka rasa manema.

Kara karanta wannan

Yarbawa Sun Fara Kuka da Tinubu Kan Yawan Fifita Legas Wajen Nada Mukamai

Kwankwasiyya
Wasu 'Yan matan Kwankwasiyya Hoto: Idon Mikiya
Asali: Facebook

Kamar yadda aka gani a wani bidiyo da ya zagaya shafukan sada zumunta, wannan mata ta shaida cewa takwarorinta sun dauko abin da zafi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Dukkanmu; da zaurawan da ‘yan matan mun zabi wadanda za mu aura idan Allah (SWT) Ya so, ko su aka aura mana, an wadatar da mu."

Su wanene ku ke so?

"Kamar ‘yan takaran da mu ka yi wa aiki, irinsu Abdulrahman Kawu Sumaila, ‘dan majalisar tarayya, Dr. Ghali Albasu da dai sauransu.
Kowa da wanda ta ke so… da su Yusuf Imam (Ogan Boye).
Mu ko wannan aka yi mana, an riga an gama wadatar da mu. Idan Allah ya so, mu na tunanin ba za su watsa mana kasa a cikin ido ba."

- Shafa’atu Ahmad

Shafa’atu ba ta iya fadin wanda ta ke kauna a cikin 'yan siyasar nan ba, amma ta tabbatar da wata Alisha ta na kaunar Sanata Sumaila.

Kara karanta wannan

An Yi Son Kai: Majalisa Za Ta Binciki Duka Mukaman da Aka Bada a Mulkin Buhari

"Ban da Madugu da Gwamna"

A cikin jagororin na Kwankwasiyya, akwai wadanda ba a tabawa, daga ciki har da Rabiu Kwankwaso, wanda ta ce shi ne madaurin aurensu.

Haka zalika babu bazawarar da ta isa ta nemi Mai girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa watau Aminu Abdussalam Gwarzo.

Abin ban mamaki, wannan Baiwar Allah ta ce a kungiyarsu akwai wanda ta ke so ta auri shugaban Hisbah da kan shi, Sheikh Aminu Daurawa.

Mata da matasa sun samu mukami a Katsina

Rahoto ya zo cewa Mai girma Dikko Umaru Radda ya aikawa Majalisa sunan Yusuf Rabiu Jirdede mai shekara 34 a cikin jerin Kwamishoninsa.

A Katsina, akwai mata uku; Fadila Muhammad Dikko, Hadiza Yaradua da Zainab Musawa Musawa da ake sa ran za su zama Kwamishinoni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel