Matar Aure Ta Yi Wa Dan Cikinta Wanka Da Tafasashshen Ruwa Bayan Ya Kawo Budurwarsa Gida a Jihar Cross Rivers

Matar Aure Ta Yi Wa Dan Cikinta Wanka Da Tafasashshen Ruwa Bayan Ya Kawo Budurwarsa Gida a Jihar Cross Rivers

  • Wata matar aure a jihar Cross Rivers ta hukunta ɗan cikinta bayan ya kawo mata budurwarsa cikin gida
  • Matar auren wacce ba ta gamsu da wannan ɗabi'ar ta sa ba, ta fusata inda ta tafasa ruwan zafi ta yi masa wanka da shi
  • An garzaya da matashin zuwa asibiti domin duba lafiyarsa sakamakon munanan raunikan ƙuna da ya samu a jikinsa

Jihar Cross Rivers - Wata matar aure mai suna Maryam Zakari, ta yi wa ɗan cikinta mai suna Babanne Abdullahi wanka da tafasashshen ruwan zafi bayan ya kawo budurwarsa gida a jihar Cross Rivers.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Maryam ta tafasa ruwan zafin ne wanda ta yi amfani da shi wajen ƙwararawa a jikin Babanne, a ranar Alhamis da ta gabata, wanda hakan ya sanya ya samu munanan raunika.

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Abba Gida-Gida Ya Lashi Takwabin Aurar Da 'Yar Da TikTok Murja Kunya

Matar aure ta yi wa dan cikinta wanka da tafasashshen ruwa
Matar aure ta hukunta dan cikinta bayan ya kawo budurwa gida Hoto: Thenation.com
Asali: UGC

Lamarin ya auku ne a unguwar Bogobiri, ta Hausa-Fulani da ke cikin birnin Calabar, babban birnin jihar.

Shaidu sun ba da bayani

Wani shaidar ganau ba jiyau ba mai suna Dauda, ya bayyana cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ta ga yaron ne tare da budurwarsa a cikin ɗakinsa, a maimakon ta yi masa gargaɗi da baki, sai ta yanke shawarar kwarara masa ruwan zafi. Ta kwarara masa ruwan zafin a jikinsa sannan ta fara kururuwar neman taimako."

Lokacin da wakilin jaridar ya isa gidansu Babanne, mutane da yawa sun taru a wajen, inda da yawa daga cikinsu su ke nuna wa matar abin da ta yi ba ta kyauta ba.

"Ba wai maganar kawo budurwar ba ce kawai ta sanya ta aikata masa hakan, amma saboda bai kawo mata abin da ya ke samu a kullum inda yake ba budurwarsa." A cewar Dauda.

Kara karanta wannan

Subhanallahi: Rayuka Da Dama Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsari Da Ya Auku a Wata Jiha

An garzaya da Babanne zuwa wani asibitin kuɗi a birnin Calabar domin duba lafiyarsa.

Menene abin da ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Irene Ugbo, ta bayyana cewa ba a kawo mata rahoto kan lamarin ba.

Ƙoƙarin jin ta bakin iyayen Babanne ya ci tura domin sun ƙi yarda a tattauna da su.

Saurayi Ya Aika Hoton Tsohuwar Budurwarsa Tsirara

A wani labarin kuma, wani saurayi a jihar Edo ya shiga hannun jami'an ƴan sanda bayan ya aika hoton tsohuwar budurwarsa tsirara ga mai shirin aurenta.

Saurayin ya aikata wannan ɗanyen aikin ne saboda tsananin kishin da yake na tsohuwar sahibarsa za ta yi aure ta rabu da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel