Za’a yi auren zaurawa 3,000 a jihar Kano

Za’a yi auren zaurawa 3,000 a jihar Kano

- Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin mutum 23 akan auren zawarawa 3,000 da za’a gudanar a jihar

- Hakan na kunshe ne a wata sanarwa daga kwamishinan bayanai na jihar, Malam Mohammed Garba

- Gwamnan jihar, Dr Abdullahi Ganduje ya amince da kafa kwamitin ba tare da bata lokaci ba

Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin mutum 23 akan auren zawarawa 3,000 da za’a gudanar a jihar.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa daga kwamishinan bayanai na jihar, Malam Mohammed Garba a Kano a ranar Laraba, 12 ga watan Disamba.

Ya bayyana cewa gwamnan jihar, Dr Abdullahi Ganduje ya amince da kafa kwamitin ba tare da bata lokaci ba.

Yace an umurci kwamitin mutum 23 da su tantance tare da zabar wadanda za su amfaa daga kananan hukumomi 44 na jihar.

A cewar Garba, mambobin kwamitin harda Farfesa Sani Zahraddeen, limamin babban masallacin juma’a na Kano.

Za’a yi auren zaurawa 3,000 a jihar Kano
Za’a yi auren zaurawa 3,000 a jihar Kano
Asali: Depositphotos

Sauran mambobin sun hada da: Ustaz Ali Baba Muhammad, mai a gwamna shawara kan harkokin addini, Alhaji Murtala Sule-Garo, kwamishinan harkokin kananan hukuma da sarauta.

Har ila yau a kwamitin akwai Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Karaba, shugaban kwamitin Shura, Sheikh Yusuf Gambari, Sheikh Tijjani Zangon-Barebari, shugaban hukumar shari’ar, Malam Sani Abdullahi Tofa, Darakta Janar na hukumar Shari’a da kuma Sheikh Ibrahim Shehu Mai Hula shugaban hukumar Hisbah.

KU KARANTA KUMA: Za a fara daure Barayin kayan wuta na tsawon shekaru 7 a gidan yari

Sauran sun hada da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, kwamanda janar na hukumar Hisah, Malam Abdurrahman Abba Sufi, Darakta-Janar na hukumar Hisbah, Dr Abdullahi Saleh Pakistan and Dr Malama Zahra’u Muhammad, mataimakiyar kwamanda janar na hukumar Hisbah.

Sauran mambobin da aka nada sune Malama Fatima Muhammad Fagge, Malam Usman Yusuf Makwarari, shugaban hukumar Zakkah da Hubsi, Malam Safiyanu Ibrahim Gwagwarwa, Darakta Janar na hukumar Zakkah da Hubsi, Mustapha Hamza Buhari, mai ba gwamna shawara akan harkokin siyasa.

Sauran sune Dr Tahir Adam Baba Impossible, Dr Aminu Ibrahim, Hajiya Bilkisu Saleh, Dr Maryam Sulaiman, Dr Hauwa Muhammad, Dr Ashiru Rajab, SACA, Kano, Abdullahi Balarabe, DAGS, sakataren hukumar lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel