Sojoji 36 Na Neja: Za Mu Dau Fansar Kisan Mutanenmu, In Ji Shugaban Tsaro Christopher Musa

Sojoji 36 Na Neja: Za Mu Dau Fansar Kisan Mutanenmu, In Ji Shugaban Tsaro Christopher Musa

  • Rundunar tsaron Najeriya ta ce za ta ɗauki fansar sojoji 36 da 'yan ta'adda suka kashe a jihar Neja
  • Shugaban rundunar tsaton, Janar Christopher Musa ne ya bayyana hakan yayin binne wasu daga cikin sojojin a Abuja
  • Ya bai wa 'yan uwan mamatan tabbacin cewa jinanen 'yan uwansu ba za su tafi a banza ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban rundunar tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa Gwabin, ya ce za su ɗauki fansar jinanen jami'ansu 36 da 'yan ta'adda suka kashe a jihar Neja.

Legit.ng ta yi rahoto a baya kan yadda 'yan bindiga suka yi wa sojojin Najeriya kwanton ɓauna a tsakanin Zungeru zuwa Tegina da ke jihar Neja, gami da kuma ɓaron jirgin sojin saman Najeriya.

Christopher Musa ya ce za su ɗauki fansa kan sojojin da aka kashe
Babban hafsan tsaro ya ce za su ɗauki fansar sojojinsu da 'yan ta'adda suka kashe a Neja. Hoto: Chris Gwabin Musa
Asali: Facebook

Ba za su tafi a banza ba, za mu ɗauki fansa - Musa

Kara karanta wannan

Jimami: 'Yan Bindiga Sun Bindige Soja 1 Tare Da Yin Awon Gaba Da Maƙudan Kuɗaɗe

Janar Christopher Musa ya bayyana hakan ne a wajen binne wasu daga cikin gawarwakin sojojin da 'yan ta'addan suka kashe a maƙabartar sojoji da ke Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Musa ya ce babu wanda za su ƙyale daga cikin 'yan ta'addan, inda ya ce za su bi su duk inda suke domin ɗaukar fansar mutanensu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma taya 'yan uwan sojojin da suka rasa rayukan na su jimami, inda ya ƙara tabbatar mu su da cewa jinanen 'yan uwansu ba za su tafi a banza ba.

Sojoji 20 ne aka binne a maƙabartar ta Abuja

A ranar Juma'a, 25 ga watan Agusta ne dai aka binne gawarwakin 20 daga cikin sojojin da aka kashe waɗanda aka ɗauko daga Kaduna zuwa maƙabartar sojojin kamar yadda Premium Times ta wallafa.

Kara karanta wannan

Kaico: 'Yan Bindiga Sun Bindige Malamin Addini Har Lahira a Jihar Kaduna

Hakan wata alama ce ta girmamawa daga gidan soji ga irin gudummawar da sojojin suka bai wa ƙasarsu a lokacin da suke a raye.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron binne sojojin baya ga shugaban rundunar tsaron, akwai babba da ƙaramin ministan tsaro wato Muhammed Badaru da Bello Matawalle.

Haka nan ma iyalai da sauran 'yan uwan mamatan sun samu zuwa binne gawarwakin sojojin.

NAF za ta samu ƙarin jiragen yaƙi 18

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan bayanin da rundunar sojin saman Najeriya (NAF), ta yi na cewa za ta samu ƙarin jiragen yaƙi 18 daga ƙasashen Amurka da Turkiyya.

Shugaban hukumar sojin saman AM Abubakar Hassan ne ya bayyana hakan, inda ya ce za su yi amfani da jiragen wajen fatattakar 'yan ta'addan da suka addabi Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel