Badaru, Matawalle Sun Samu Halartar Binne Gawarwakin Sojoji Da Su Ka Mutu A Neja

Badaru, Matawalle Sun Samu Halartar Binne Gawarwakin Sojoji Da Su Ka Mutu A Neja

  • A makon daya gabata, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kisan sojojinta 36 da 'yan bindiga su ka yi a jihar Neja
  • Rundunar ta ce hakan ya biyo bayan kwanton bauna da 'yan bindigan su ka yi wa sojojin da kuma kado jirgin saman rundunar
  • A yanzu haka ana bikin binne sojojin a jihar Neja inda ministan tsaro da mataimakinsa su ka samu halarta

Jihar Neja - A yanzu ana bikin binne gawarwakin sojoji akalla 20 da 'yan bindiga su ka yi ajalinsu a jihar Neja.

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojojinta 36 a makon daya gabata.

An kammala binne gawarwakin sojojin da suka mutu a Neja
Badaru, Matawalle Sun Halartaci Binne Sojoji Da Su Ka Mutu A Neja. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Yaushe aka kashe sojojin?

Wannan na zuwa ne yayin da 'yan bindiga su ka musu kwanton bauna a hanyar Zungeru zuwa Tegina da kuma kado jirgin sojin da 'yan bindiga su ka yi.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: ECOWAS Ta Tura Sakon Karshe Ga Sojin Nijar, Ta Ce Su Na Da Sauran Dama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta tattaro cewa yanzu haka ana kan binne sojojin inda ministan tsaro, Badaru Abubakar ya samu halarta.

Sauran wadanda su ka halarta akwai karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da hafsan rundunar tsaro, Janar Christopher Musa, cewar PM News.

Jerin sunayen sojojin da ake binnewa a yau.

1. Marigayi Manjo SA ONI

2. Marigayi Laftanar ANTHONY DURYUMSU

3. Marigayi Laftanar IBRAHIM ADAMU

4. Marigayi Laftanar GM ODUSAMI

5. Marigayi Laftanar US ALKALI

6. Marigayi Sajen FARUK MOHAMMED

7. Marigayi IBRAHIM GARBA

8. Marigayi CHIROMA POGU

9. Marigayi ADAMA ISAAC

10. Marigayi HARUNA JAMILU

11. Marigayi SAMAILA BASHIRU

12. Marigayi AB SULEIMAN MK (sojan ruwa)

13. Marigayi JAURO AMOS (sojan sama)

14. Marigayi SUNDAY OKOPI

15. Marigayi EKPANYO EDETD

16. Marigayi ALARIBE DANIEL (sojan sama)

17. Marigayi BRIGSS STEPHEN (sojan sama)

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Saki Miliyan 854 Don Auren Zawarawa a Jihar Kano, Zai Kuma Aiwatar Da Wasu Muhimman Ayyuka 2

18. Marigayi YAKUBU AYUBA

19. Marigayi NURA MOHAMMED

20. Marigayi HABIB ALIYU

21. Marigayi TANKO WAJE

22. Marigayi ABUBAKAR ABDULRAHAMAN (sojan sama)

Sojoji Sun Bayyana Yawan Jami'ansu Da Aka A Neja

A wani labarin, rundunar tsaro a Najeriya ta bayyana cewa 'yan bindiga sun kashe akalla jami'ansu guda 36 a jihar Neja.

Rundunar ta bayyana haka ne a ranar 17 ga watan Agusta a Abuja.

Ta ce kisan sojin na zuwa ne bayan 'yan bindiga sun yi musu kwanton bauna da kuma wadanda su ka kado a jirgin sama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel