'Yan Bindiga Sun Halaka Wani Fasto Yayin Da Yake Aiki a Gonarsa a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Halaka Wani Fasto Yayin Da Yake Aiki a Gonarsa a Kaduna

  • Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun halaka wani babban Fasto a Kaduna
  • 'Yan bindigar sun halaka Faston mai suna Jeremiah Mayau a yayin da ya je gonarsa da ke garin Kujama
  • Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Kaduna, Joseph Hayab ne ya bayyana hakan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Chikun, jihar Kaduna - Wasu 'yan bindiga sun kashe Jeremiah Mayau, Faston Tawaliu Baptist Church da ke Kujama, ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) na jihar Kaduna, Joseph Hayab ne ya tabbatar da hakan ranar Alhamis a Kaduna kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Yan bindiga sun kashe Fasto a Kaduna
'Yan bindiga sun halaka Fasto a jihar Kaduna. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Yadda 'yan bindiga suka halaka babban Fasto a Kaduna

Joseph Hayab ya bayyana cewa mummunan lamarin ya faru ne da yammacin ranar Larabar da ta gabata yayin da Faston ya je gonarsa da ke garin Kujama ta ƙaramar hukumar Chikun.

Kara karanta wannan

An Kuma Yin Juyin Mulki a Wata Kasar Afrika Ta Yamma Ta Daban? Bayanai Sun Fito

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce akwai ciwo matuƙa, yadda 'yan ta'adda ke shiga duk inda suka ga dama ba tare da wani ya iya tanka mu su ba duk kuwa da tarin hukumomin da ake da su.

Ya ƙara da cewa masu riƙe da madafun iko sun ƙo yin abinda ya kamata wajen magance matsalar ta yanda babu wanda ya isa ya ɗaga mu su yatsa.

Hayab ya ɓuƙaci jami'an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen hare-haren 'yan ta'adda a faɗin jihar baki ɗaya kamar yadda New Telegraph ta wallafa.

Sojoji sun yi musayar wuta da 'yan daba a Ebonyi

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan burtun da sojoji suka sha da wasu 'yan daba a ƙauyen Effium da ke a ƙaramar hukumar Ohaukwu ta jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Babbar Buƙatar Yan Bindiga a Jihar Zamfara Ta Bayyana, Ɗan Majalisa Ya Tono Gaskiya

'Yan daban dai sun zo ƙauyen ne ɗauke da manyan makamai inda suka kora mutane sannan suka yi yunƙurin tafka sata a wata coci.

Sai dai sojojin da ke bakin aiki sun ƙalubalancin 'yan daban, wanda hakan ya haddasa musayar wuta a tsakaninsu.

Dan bindiga ya halaka mutane 3 a wani gidan giya

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan harin da wani ɗan bindiga ya kai wata mashayar giya da ke jihar California ta ƙasar Amurka.

A yayin harin, ɗan bindigar ya yi harbin kan mai uwa da wabi, inda nan take ya halaka mutane uku tare da jikkata Wasu mutanen shida, kafin daga bisani shi ma ya rasa ransa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel