Hukumar NAF Za Ta Samu Karin Jiragen Yaki 18 Domin Fatattakar 'Yan Ta'adda

Hukumar NAF Za Ta Samu Karin Jiragen Yaki 18 Domin Fatattakar 'Yan Ta'adda

  • Hukumar sojojin saman Najeriya ta bayyana cewa tana shirin karɓar sabbin jiragen yaƙi guda 18
  • Shugaban hukumar AM Abubakar Hassan ya tabbatar da cewa jiragen yaƙin za su iso ne daga ƙasashen Amurka da Turkiyya
  • Abubakar ya ƙara jaddada cewa jiragen yaƙin za su ƙara taimakawa hukumar wajen fatattakar ƴan ta'adda a faɗin ƙasar nan

Jihar Rivers - Shugaban hukumar sojojin saman Najeriya (CAS), AM Hassan Abubakar, ya bayyana cewa nan bada daɗewa ba hukumar za ta samu ƙarin jiragen yaƙi 18 domin faɗaɗa jiragen yaƙinta.

Abubakar ya bayyana hakan ne a wajen wani rangadin kwana a ɗaya na duba dakarun hukumar na 'NAF 115 Special Operations Group' (SOG), a birnin Fatakwal na jihar Rivers, ranar Laraba, cewar rahoton Daily Trust.

Hukumar sojojin sama na dab da samun karin jirage
Shugaban hukumar sojin saman Najeriya, AM Hassan Abubakar Hoto: @NigAirForce
Asali: Twitter

The Nation ta ce Shugaban ya bayyana cewa jiragen yaƙi masu saukar ungulu guda 12 za a kawo daga ƙasar Amurka, yayin da gwamnatin ƙasar Turkiyya za ta bayar da wasu jiragen masu saukar ungulu guda shida a watan Satumba.

Kara karanta wannan

Shugaban Hukumar Sojojin Sama Ya Ziyarci Iyalan Matukan Jirgin Saman Da Suka Yi Hatsari, Ya Yi Wani Muhimmin Alkawari

Jiragen yaƙin na dab da isowa

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abubuwan da suka faru a ƴan kwanakinnan ba za su sare mana gwiwa ba domin gwamnatin tarayya ta amince da siyo jirage 12 na AH1 Zulu Cobra da jirage guda shida masu saukar ungulu na T129, daga ƙasashen Amurka da Turkiyya."
"Eh tabbas, mun yi baƙin cikin asarar jirginmu (MI 171) da muka yi, amma akwai jirage masu yawa da za su iso domin ƙara ƙarfin yadda mu ke gudanar da ayyukanmu."

Dalilin ziyarsa zuwa jihar

Abubakar ya bayyana cewa ya ziyarci jihar ne domin yin ta'aziyya ga iyalan matuƙan jirgin saman hukumar da suka rasu a hatsarin jirgin da ya auku a jihar Neja a ranar 14 ga watan Agusta.

"Eh mun zo nan ne domin ta'aziyya iyalan sojojin da muka rasa a hatsarin jirgin." A cewarsa.

Kara karanta wannan

"Akwai Babbar Matsala" Fitaccen Malami Ya Bayyana Hukuncin da Kotu Zata Yanke Kan Nasarar Tinubu a 2023

Dalilin Hatsarin Jirgin NAF

A wani labarin kuma, shugaban hukumar sojojin saman Najeriya, AM Hassan Abubakar ya bayyana dalilin da ya sanya jirgin saman hukumar ya yi hatsari a jihar Neja.

Abubakar ya bayyana cewa sauyin yanayin da aka samu na yawan giragizai a sararin samaniya waɗanda ke kare abin da matuƙan jirgin za su iya hangowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel