Yan Bindiga Sun Bukaci Naira Miliyan 4 Kudin Fansa Ga Matashiya Mai Bautar Kasa, NYSC A Zamfara
- ‘Yan bindiga a jihar Zamfara sun bukaci Naira miliyan hudu a matsayin kudin fansa na daya daga cikin matasa masu bautar kasa
- An sace matasan ne a jihar Zamfara yayin da su ke kokarin zuwa jihar Sokoto daga birnin Uyo ta Akwa Ibom
- Daya daga cikin mahaifin matasan, Emmanuel Etteh ya tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun kira shi kan biyan kudin
Jihar Zamfara – ‘Yan bindiga sun bukaci kudin fansa na Naira miliyan 4 kan daya daga cikin masu bautar kasa da suka sace a jihar Zamfara.
‘Yan bindigan sun sace wasu matasa masu bautar kasa, NYSC guda takwas a makon da ya gabata yayin da su ke kokarin zuwa sansanin horaswa na hukumar.
Yaushe aka sace 'yan bautar kasar, NYSC?
Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Tsinci Gawar Shugabar Alkalai a Yanayi Mara Kyau a Jihar Arewa
Rahotanni sun tattaro cewa an sace masatan ne da su ke cikin bas ta AKTC wanda su ka fito daga Uyo cikin jihar Akwa Ibom zuwa jihar Sokoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mahaifin daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su, Emmanuel Ette ya bayyana cewa ‘yarsa Glory Thomas na daga cikin wadanda aka kaman.
Ya bayyana wa gidan talabijin na Channels cewa tabbas ‘yan bindigan sun bukaci har Naira miliyan hudu a matsayin kudin fansa.
Etteh ya ce sun kira shi da lambarsu inda su ke bayyana masa sace ‘yar tasa da cewa zai biya Naira miliyan hudu a matsayin kudin fansa.
Ya ce:
“Sun kira ni da lambarsu tare da cewa zan biya Naira miliyan hudu a matsayin kudin fansa.
“Na yi magana da ‘yata inda na tambaye su ta yaya za a biya kudin, sai su ka ce mu tuntubi AKTC.”
Meye mahaifin matashiyar NYSC ya ce?
Mahaifin ya bayyana cewa tun daga wannan lokacin bai sake jin duriyarsu ba dangane da yaran inda ya ce bai sani ba ko sun sake su, Naija Times ta tattaro.
Rundunar ‘yan sanda a jihar ba ta ce komai ba dangane da wannan lamari har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.
Yayin da tun farko rundunar sojin Najeriya ta umarci jami’ansu da su bazama cikin dazuka neman ‘yan bindigan tare da ceto matasan ba tare da sun samu rauni ba.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Masu Bautar Kasa, NYSC
A wani labarin, 'yan bindiga sun yi garkuwa da matasa masu bautar kasa su takwas a Zamfara.
'Yan bindigan sun musu kwanton bauna ne yayin da su ke cikin bas daga jihar Akwa Ibom zuwa Sokoto.
Asali: Legit.ng