Benue: An Halaka Tsohuwar Shugabar Kotun Kostumare a Jihar Benuwai

Benue: An Halaka Tsohuwar Shugabar Kotun Kostumare a Jihar Benuwai

  • An shiga tashin hankali yayin da aka tsinci gawar wata shugabar Alkalai da ta yi ritaya a jihar Benuwai, Misis Margaret Igbeta
  • Rahoto ya nuna an gano gawar mamaciyar a gidanta da ke cikin kwaryar birnin Makurdi cikin yanayi mara kyau ranar Alhamis
  • Jami'an yan sanda sun fara bincike domin kama waɗanda suka aikata wannan ɗangen aiki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Benue state - Rahotanni sun bayyana cewa an kashe tsohuwar shugabar Kotun ɗaukaka ƙara ta Kotumare, Misis Margaret Igbeta a gidanta da ke layin Wantor Kwange, Makurdi.

Mai shari'a Igbeta, yar kimanin shekaru 72 a duniya, an tsinci gawarta cikin jini a gidanta da ke kwaryar babban birnin jihar Benuwai ranar Alhamis da daddare.

Taswirar jihar Benuwai.
Benue: An Halaka Tsohuwar Shugabar Kotun Kostumare a Jihar Benuwai Hoto: dailytrust
Asali: UGC

An tattaro cewa da safiyar ranar Juma’a aka gano gawar alkalin bayan wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe ta kana suka zubar da jininta a kusan ko ina a gidan.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Harin Gidan Kwanan Ɗalibai Mata a Jami'ar Najeriya, Sun Tafka Ta'adi

Daily Trust ta ce ana zargin cewa watakila an kashe marigayya mai shari'a ne kwana daya da ya gabata duba da yadda yanayin gawar ta ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga baya ‘yan sanda sun dauko gawar ta daga gidanta, wanda ke daura da kwalejin likitanci ta BSU kusa da titin Gboko a cikin garin Makurdi.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

A rahoton Tribune, wata Majiya daga cikin hukumar ‘yan sanda, wacce ba ta da izinin yin magana da ‘yan jarida kan batun, ta ce:

"Eh gaskiya ne. Jiya, (Alhamis) aka gano gawar ta a gidanta cikin wani yanayi mara kyau, ma'ana ba jiya lamarin ya faru ba, wataƙila kwana daya kafin jiya (Laraba)."

Majiyar ta kara da cewa ‘yan sanda na kokarin bankado wadanda suka kashe alkalin duk da cewa ‘yan uwanta sun riga sun ba da bayanai masu amfani da zasu taimaka wajen kama su.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Shari’a Ta Bai Wa Magidanci Masauki a Gidan Yari Kan Lakadawa Tsohuwar Matarsa Duka

Lokacin da aka tuntuɓi jami’ar hulda da jama’a ta ‘yan sanda jihar (PPRO), SP Catherine Anene, ta amsa da cewa, “Ku bari na koma garin na binciko ainihin abin da ya faru.”

Yan Bindiga Sun Kai Hari Dakunan Kwanan Dalibai Mata a Jami'a

A wani labarin na daban kuma Wasu mahara ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki gidan kwanan ɗalibai mata a jami'ar jihar Ribas.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigan sun jikkata wasu ɗalibai mata a harin, lamarin da ya haifar da zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel