Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Matasa Masu Bautar Ƙasa NYSC

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Matasa Masu Bautar Ƙasa NYSC

  • Miyagun 'yan bindigan jeji sun yi garkuwa da matasa 'yan bautar ƙasa 8 a hanyarsu ta zuwa jihar Zamfara
  • Rahotanni sun nuna cewa 'yan bautar ƙasan sun taso ne tun daga Uyo, jihar Akwa Ibom, suka bi ta Sakkwato kafin shiga Zamfara
  • Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sandan Zamfara, Yazid Abubakar, ya nemi a ba shi lokaci ya tabbatar da lamarin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Zamfara State - Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) 8 a kan wata babbar hanya a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma.

Baki ɗaya 'yan bautar ƙasar da lamarin ya shafa suna cikin wata motar Bas AKTC kuma sun fito ne daga Uyo, jihar Akwa Ibom, suka shiga ta Sakkwato a hanyarsu ta zuwa Zamfara.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Harbe Kwamandan Rundunar Tsaro Har Lahira a Jihar Arewa

Yan bindigan jeji sun sake sace mutane a Zamfara.
Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Matasa Masu Bautar Ƙasa NYSC Hoto: premiumtimes
Asali: Twitter

Bayanai sun nuna cewa matasan 'yan bautar kasar sun shiga hannun 'yan bindiga ne a hanyar zuwa Zamfara domin gudanar da aikin hudimta wa kasa wanda aka fi sani da NYSC.

Wata majiya daga kamfanin sufurin motocin AKTC ta tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar Premium Times da safiyar ranar Litinin, 21 ga watan Agusta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutumin, wanda ya nemi a sakaya bayanansa saboda ba shi da hurumin magana kan lamarin, ya ce masu bautar kasan su 11 ne a motar amma uku sun yi nasarar tsere wa 'yan bindigan.

Ya ce bayan 'yan bautar ƙasa, maharan sun haɗa da direban motar Bas ɗin sun yi awon gaba da su zuwa cikin jeji.

A cewarsa, "Baki ɗaya suka kwashe 'yan bautar ƙasan da ke cikin motar suka tasa ƙeyarsu zuwa cikin daji. Daga baya 'yan sanda suka je suka ɗauko Motar."

Kara karanta wannan

Hankula Sun Tashi A Babban Birnin Jihar Kudu Yayin Da Yan Bindiga Suka Kashe Tsohon Dan Sanda Da Matarsa

"Sun baro Uyo ranar Jumu'a, suka kwana a Abuja. Wshe gari, yayin da suka wuce zuwa Sakkwato ne suka faɗa tarkon masu garkuwa da mutane."

Wane mataki aka ɗauka kan lamarin?

Ya ce tuni aka kai rahoton sace mutanen ga gwamnati da kuma hukumomin tsaro domin ɗaukar matakan kubutar da matasan, jaridar Gazette ta tattaro.

Yayin da aka tuntuɓi jami'in hulɗa za jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya ce zai bincika sahihancin lamarin kafin ya yi magana.

Sanatan Ogun Ta Tona Asirin Waɗanda Suka Hallaka Babban Hadiminsa

A wani rahoton kuma Sanata mai wakiltar Ogun ta yamma a inuwar APC, Solomon Adeola, ya bayyana waɗanda suka kashe hadiminsa a Legas.

An harbe Mista Sanni ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida, sannan aka jefar da gawarsa a kusa da wani barikin sojoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel