Abba Gida-Gida Ya Ware Miliyan 700 Don Biyawa Daliban Kano Kudin Makaranta a BUK

Abba Gida-Gida Ya Ware Miliyan 700 Don Biyawa Daliban Kano Kudin Makaranta a BUK

  • Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da ware naira miliyan 700 don biya wa daliban BUK kudin makaranta
  • Hakan yana daga cikin kokarin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na ragewa yan jiharsa radadin matsin tattalin arzikin da ake ciki
  • Ya ce nan gaba kadan za su fitar da tsarin biyan kudin inda dalibai 7000 za su ci gajiyar shirin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta amince da sakin kudi naira miliyan 700 domin biya wa dalibai 7,000 yan asalin jihar da ke karatu a jami'ar Bayero, BUK kudin makaranta.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Albashi Da Allawus Din Ministocin Tinubu Ya Bayyana, Za Su Lakume Biliyan 8.6

Abba Gida-Gida ya amince da biyan kudin makarantar daliban BUK 7000
Abba Gida-Gida Ya Ware Miliyan 7000 Don Biyawa Daliban Kano Kudin Makaranta a BUK Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Ku tuna cewa gwamnatin jihar Kano ta hannun kwamishinan ilimi na jami'a, Dr. Yusuf Kofar Mata, ta hada kai da BUK kan matakan rage kaso 100 na karin kudin makarantar da aka yi wanda ake ganin zai yi sanadiyar da dalibai da dama za su bar makaranta.

Hakazalika, hukumomin jami’ar a wani mataki na magance karin kudaden da suka ce ya zama dole idan aka yi la’akari da yadda ake kashe su, sun kafa tsarin bayar da tallafin karatu kyauta ta hanyar bayar da kudaden gudanar da jami’o’in da aka samu daga masu hannu da shuni.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka kuma, an tsawaita lokacin rijista da wata daya domin ba iyaye da dalibai damar biyan kudin makaranta.

An ware miliyan 700 don ragewa dalibai radadin halin da ake ciki, gwamnan Kano

Gwamnan ya kuma ce an amince da fitar da miliyan 700 na biyan kudin makarantar daliban na BUK a taron majalisar zartarwa na jihar wanda aka yi a ranar Laraba, duba da matsin rayuwa a kasar.

Kara karanta wannan

Sababbin Ministocin Najeriya da Aikace-Aikacen da Shugaban Kasa Tinubu ya ba su

Ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da hanyoyin biyan kudin.

Ya rubuta a shafin nasa:

“Daga cikin kokarinmu na rage radadin matsin da tattalin arzikinmu ke ciki a yanzu; Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano karkashin jagorancina a yau, ta amince da sakin naira miliyan dari bakwai don biya wa daliban jami’ar Bayero (BUK) 7000 kudin makaranta.
“Za a sanar da karin bayani kan yadda za a tafiyar da tsarin nan gaba. – AKY.”

Gwamnatin Abba Gida-Gida ta gano makaranta mai dalibai 5,000 da babu azuzuwa

A wani labarin, mun ji cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ta koka kan yanayin da ta tarad da ɓangaren ilimi a jihar.

Gwamnatin ta bayyana cewa akwai makarantar da ta gano mai ɗalibai 5,000 amma babu azuzuwa da kuma ingantaccen makewayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel