An Sauya Zane, Davido Ya Saki Sabon Bidiyon Wakar da a Baya Ya Jawo Cece-Kuce a Twitter

An Sauya Zane, Davido Ya Saki Sabon Bidiyon Wakar da a Baya Ya Jawo Cece-Kuce a Twitter

  • Yanayi ya sake kunno kai yayin da Davido ya sake sakin bidiyon wakar ‘Jaye Lo’ da ta jawo cece-kuce a kwanakin baya
  • A baya mun ruwaito muku yadda wakar ya jawo martani mai zafi daga al’ummar Musulmi bayan sakin yankin wakar
  • A halin da ake ciki, an ga yadda aka yanke wasu bangarori daga cikin wakar, wanda yake nuna an yi gyara a aikin wakar

Najeriya - Shahararren mawakin nan Davido, ya fitar da sabon bidiyon wakar yaronsa da ya jawo cece-ku ce a kwanakin baya a kafar sada zumunta mau suna 'Jaye Lo'.

Davido ya gamu da fushin al’ummar Musulmi a a watan da ya gabata lokacin da ya fara fitar da wani gutsure daga wakar ta ‘Jaye Lo’ a shafinsa na Twitter.

Shahararren mawakin ya sha suka daga Musulmi musamman ‘yan Arewa masu kaunar addininsu, inda suka tarar da dago batun rashin da’a ga yadda aka wulakanta martanar sallah a wakar.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tsare Fitaccen Malamin Addini Kan Zargin Mallakar Bindiga AK-47 A Coci, Ta Bayyana Mataki Na Gaba

An sake sakin wakar Jaye Lo
Wakar da ta jawo cece-kuce ta sake dawowa | Hoto: @davido
Asali: Twitter

Yadda bidiyon ya jawo cece-kuce a Twitter

Idan baku manta ba, an ga lokacin da wasu katti ke tikar rawa bayan idar da sallah a masallaci, kana suna sanye da fararen tufafi kamar dai masu bin addinin Islama.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin bidiyon da ya yada, an ga lokacin da mutanen ke sallah, inda bayan idarwa suka kama girgiza da cashewa da rawa.

Hakanan, an ga wani a kan tufin masallaci yana rawa, inda yake sanye da farin kaya da kuma murdadden gashin ka da addinin Islama ya hana.

An yi kira ga Davido ya sauke bidiyon

A yanayin ne aka ba Davido shawarin ya gaggauta sauke bidiyon daga shafinsa tare da ba Musulmai hakuri bisa bata musu sunan addini.

A bangarensa, ya sauke goge bidiyon a shafinsa, amma sai kuma lamarin ya kara daukar zafi daga baya biyo bayan maganar da ya yi.

Kara karanta wannan

Sanatan NNPP Zai Kashe Fiye da N20m Wajen Biyawa Dalibai Kudin Karatu a Kano

A bidiyon ya sake yadawa yanzu, an ga inda aka cire wasu bangarori daga wuraren da ake yiwa kallon yiwa addinin Islama rashin da’a.

Goge bidiyon wakar da aka farko Davido ya yi

Mawaki David Adeleke da aka fi sani da Davido a karshe ya ji korafin jama'a tare da goge faifan bidiyon da ake ta cece-kuce a kai.

Wannan na zuwa bayan mawakin ya wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna rashin mutunta addinin Musulunci da yaronsa Logos Olori ya hau, da ke nuna rashin da'a ibadar Musulmai.

A ranar Asabar 22 ga watan Yuli Davido ya sha suka daga al'ummar Musulmai bayan wallafa faifan bidiyon da ke cin zarafin Musulunci a shafinsa na Twitter.

Asali: Legit.ng

Online view pixel