A Karshe, Davido Ya Goge Faifan Bidiyon Rashin Da'a Ga Musulunci Da Ake Ta Cece-kuce A Kai

A Karshe, Davido Ya Goge Faifan Bidiyon Rashin Da'a Ga Musulunci Da Ake Ta Cece-kuce A Kai

  • A karshe, mawaki David Adeleke da aka fi sani da Davido ya ji ta mutane ya goge faifan bidiyon da ya jawo cece-kuce
  • Davido ya wallafa faifan bidiyon ne inda aka gano daya daga cikin yaransa, Logos Olori ya hau kan bidiyon da ke nuna batanci ga Musulunci
  • Al'ummar Musulmi da dama sun yi Allah wadai da faifan bidiyon inda suka bukaci mawakin ya goge bidiyon tare da neman afuwa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Mawaki David Adeleke da aka fi sani da Davido a karshe ya ji korafin jama'a tare da goge faifan bidiyon da ake ta cece-kuce a kai.

Wannan na zuwa bayan mawakin ya wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna rashin mutunta addinin Musulunci da yaronsa Logos Olori ya hau, da ke nuna rashin da'a ibadar Musulmai.

Kara karanta wannan

Bidiyon Davido: Malaman Musulunci Sun Magantu, Sun Fadi Matakin Da Ya Kamata A Dauka

Mawaki Davido Ya Goge Faifan Bidiyon Da Ake Ta Cece-kuce A Kai
Mawaki Davido Ya Jawo Kace-nace Bayan Wallafa Wani Faifan Bidiyo Da Ya Ta Da Hankulan Jama'a. Hoto: Instagram.
Asali: Instagram

A ranar Asabar 22 ga watan Yuli Davido ya sha suka daga al'ummar Musulmai bayan wallafa faifan bidiyon da ke cin zarafin Musulunci a shafinsa na Twitter.

Al'ummar Musulmai sun yi Allah wadai da bidiyon na Davido

Musulmai da dama sun bayyana faifan bidiyon da cewa cin zarafi ne da kuma rashin mutunta addininsu inda aka gano matasa na sallah daga bisani suka koma rawa da waka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun zargi mawakin da rena addinin Musulunci inda ya ke hada sallah mai daraja da rawa da waka, Daily Trust ta tattaro.

Legit.ng Hausa ta tabbatar da goge faifan bidiyon bayan ziyartar shafukan sada zumunta na mawakin.

Sun bukaci Davido da ya goge wakar tare da neman afuwa a wurin al'ummar Musulmi.

Daga cikin masu ta'ammali da kafar sadarwa da suka kushe bidiyon akwai jarumin Kannywood, Ali Nuhu da Bashir Ahmad, hadimin tsohon shugaban kasa Buhari.

Kara karanta wannan

Bidiyon Rashin Da’a Ga Musulunci: MURIC Ta Caccaki Davido, Ta Bukaci DSS Da Ta Gayyaci Mawakin

Sauran sun hada tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani da sauran mutane masu tasiri a kafar sadarwa daga Arewacin kasar, cewar Daily Post.

Bashir Ahmad a shafinsa na Twitter ya ce tabbas Musulmai da dama ba su ji dadin haka ba, inda ya gargadi mawakin akan hada addini da barkwanci da rashin mutunta Musulunci.

Yadda wallafa bidiyon ya jawo cece-kuce

Ana shi wallafawar, Ali Nuhu ya bayyana rashin jin dadinsa da cewa wannan rashin mutunta addini ne.

Ya bukaci mawakin ya yi gaggawar goge faifan bidiyon tare da neman afuwar Musulmai, cewar GistReel.

Har ila yau, Shehu Sani ya shawarci mawakin da ya goge ko kuma ya gyara fasalin faifan bidiyon tare da neman afuwa.

Ya ce idan har za a ce wani bangare na magoya bayansa ba su ji dadin wani abin da ka yi ba, ya fi dacewa ya goge.

Mawakin bai ce komai ba akan bidiyon kuma bai ba da hakuri ba, amma bayan kwanaki biyu da hakan ya goge faifan bidiyon.

Kara karanta wannan

"Ku Yafe Masa": Ali Nuhu Ya Magantu Bayan Davido Ya Goge Faifan Bidiyo, Mutane Sun Yi Martani

Bashir Ahmad Ya Soki Davido Kan Bidiyon Wakar Da Ke Izgilanci Ga Ibadar Musulmai

A wani labarin, Bashir Ahmad, daya daga ciki tsoffin hadiman tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya caccaki mawaki Davido kan faifan bidiyon da ya sake na cin zarafin Musulunci.

Bashir ya bayyana cewa Musulmai suna mutunta addininsu kamar yadda suke mutunta na wasu.

Ya ce sallah ba karamar ibada ba ce a wurin Musulmi ganin yadda ita ce lokacin da suke da kusanci ga mahaliccinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.