Bashir Ahmad Ya Caccaki Davido Kan Yada Bidiyon Wakar da Ake Izgilanci Ga Ibadar Musulmai, Sallah

Bashir Ahmad Ya Caccaki Davido Kan Yada Bidiyon Wakar da Ake Izgilanci Ga Ibadar Musulmai, Sallah

  • Davido ya yada wani bidiyon da ke nuna rashin mutunta daya daga ibadun da Musulmai ke yi; Sallah
  • An ga lokacin da wasu maza ke tikar rawa jim kadan bayan da aka nuno sun yi sallah a cikin bidiyon wata
  • Bashir Ahmad ya ja hankali tare da gargadin masu batanci ga addinin Islama da su daina, ba daidai bane

Twitter - Daya daga cikin tsoffin hadiman tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya caccaki mawakin nan Davido tare da zarginsa da yada bidiyon batanci ga Muslunci.

Bashir Ahmad, ya bayyana cewa, Musulmai wasu irin mutane ne da ke mutunta addininsu da ma na wasu, don haka ba sa wasa da addininsu.

Ya bayyana hakan ne bayan da Davido ya yada wani gajeren bidiyon wata wakar da @logosolori ya rera, kamar yadda Legit.ng Hausa ta gani a shafin Twitter.

Kara karanta wannan

Za su ji a jikinsu: Davido ya yiwa Musulmai martanin gatsali bayan jawo hankalinsa ga bidiyon yiwa sallah izgili

Bashir Ahmad ya caccaki Davido
Wakar da aka yi bidiyonta liman da mamu na rawa a masallaci | Hoto: Bashir Ahmad, Davido
Asali: Twitter

Meye bidiyon ke kunshe dashi?

A bidiyon da muka gano a shafin Davido, an nuno wasu mutane suna sallah, kana daga bisani suka barke da rawa da waka sanye da sutura irinta Musulmai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan lamar ya ja hankalin jama’a, domin kuwa a addinin Islama, babu batun rawa a masallaci ko a wurin sallah.

Saboda haka, Bashir Ahmad ya jawo hankalin Davido tare da bayyana masa aininin abin da addinin Islama ya tanada.

Sakon Bashir Ahmad ga Davido

A rubutun da ya yi, Bashir ya ce:

“Akwai dalilai da yawa da ya sa kowane Musulmi ke ganin wannan abun a matsayin tsagwaron rashin mutunci, cutarwa da kuma muzantawa @davido.
“Ina zaton duk kun san cewa mu Musulmi ba mu cakuda addininmu da izgilanci ta kowace hanya, musamman Sallah, wacce aba ce mafi girma kuma ta biyu daga cikin rukunan Musulunci guda biyar.

Kara karanta wannan

Ba ma wasa da Sallah: Ali Nuhu ya yiwa Davido kalamai masu zafi kan bidiyon bata Sallah

“A cikin Sallah, Musulmai muna ganawa da Ubangijinmu, Allah, muna nuna kauna da girmamawa gare shi da rokonsa da kokarin nuna godiyarmu gare shi.
“Maganar ita ce, Sallah na kawo wa mutum kusa; fuska da fuska da Allah. Abin da muka gaskata kenan, kuma imaninmu kenan. Don Allah a mutunta hakan.
“Babu wani Musulmi da zai ga hakan a matsayin abin alfahari ko karbabben abu.”

Iraqi ta yi barazanar raba gari da Sweden saboda barin masu kone Qur'ani

A wani labarin, tun bayan kona Qur'ani mai girma a kasar Sweden, mutane da kasashe da dama ke Allah wadai da wannan aika-aika.

Kasar Iraqi ta bi sahu inda ta yi barazanar yanke alaka da Sweden Idan har aka sake kona Qur'ani a kasar.

Gargadin na zuwa ne bayan daruruwan mutane sun yi zanga-zanga a ofishin jakadancin Sweden a birnin Baghdad bayan samun bayanan cewa za a sake aikata hakan a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel