Bidiyon Batancin Davido: Malaman Addinin Musulunci Sunyi Martani, Sun Fadi Matakin Gaba

Bidiyon Batancin Davido: Malaman Addinin Musulunci Sunyi Martani, Sun Fadi Matakin Gaba

  • Tun bayan yada faifan bidiyo da Davido ya yi na wani yaronsa, ake ta cece-kuce akai musamman a Arewacin kasar
  • Mawaki Davido daga bisani ya goge bidiyon da ya yada bayan korafe-korafen jama'a akan ya goge tare da ba da hakuri
  • Wasu malamai da wakilin Legit.ng Hausa ya zanta da su sun yi tsokaci akan lamarin gwargwadon fahimtarsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Gombe - An yi ta cece-kuce akan wani faifan bidiyo da mawaki Davido ya yada a shafinsa na Twitter a makon da ya gabata.

Mawaki David Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya yada bidiyon da wani yaronsa Logos Olori ya yi.

Davido: Malaman Musulunci Sunyi Martani Sun Fadi Matakin Da Ya Kamata A Dauka
Mawaki Davido Ya Jawo Kace-nace Bayan Wallafa Wani Faifan Bidiyo Da Ya Ta Da Hankulan Jama'a. Hoto: Instagram.
Asali: Instagram

Mutane musamman a Arewacin kasar sun yi ta korafi akan faifan bidiyon inda suka bukaci Davido ya goge tare da ba da hakuri.

Wasu malamai sun yi martani akan faifan bidiyon

Kara karanta wannan

Wole Soyinka Ya Goyi Bayan Davido Kan Bidiyon 'Jaye Lo': "Rawa a Gaban Masallaci Ba Tsokana Bane, Kada Ka Bada Hakuri"

Sun bayyana hakan da isgilanci da cin zarafin Musulunci da kuma rashin mutunta addinin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wakilin Legit.ng Hausa ya nemi tsokacin wasu masana akan wannan lamari da ke faruwa.

Mallam Muhammad Umar wanda lakcara ne a jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Kashere a jihar Gombe ya yi tsokaci akan lamarin.

Ya ce tabbas zai yiyu ya aikata hakan ne a rashin sani, tunda ko Musulmi zai aikata hakan don neman ya burge jama'a amma a rashin sani.

Ya koka kan yadda mutane ke saurin yada abu ba tare da sun fahimci ainihin dalilin faruwar lamarin ba.

Ya ce addinin Musulunci ya haramta kida da waka da saboda a addinance mawaka batattun mutane ne ke binsu.

Ya ce:

"Toh lallai abin da ya aikata din watakila ya yi hakan ne a rashin sani.
"Kasan mutumin da ba ya cikin addini, ko wani Musulmin ma zai iya aikata haka don burge mutane, toh kasan mutanen mu da daukar abu da zafi tare da yadawa ba tare da an fahimci ainihin abin ba."

Kara karanta wannan

Abin Duniya Ya Jawo Rigima Tsakanin Mashahurin ‘Dan Kasuwan Najeriya da Yaransa

Ya kara da cewa:

"Abin da ya kamata Musulmi su yi shi ne daman mafi yawan masu sauraronsa irinsa ne, toh ya kamata a masa uzuri a ji daga bakinsa manufarsa akan abin.
"Idan mummuna ce, toh sai a dauki mataki kamar idan kana bibiyarsa a shafukansa sai ka daina da sauran matakai makamantan haka.
"Kamar yanzu da aka ce ya goge kaga watakila ya razana ne da cewa ashe ya yi don ya burge ne kuma ga yadda abin ya dawo, ashe bai burge ba."

Ana shi tsokacin, Sheikh Musa Yusuf Asadus Sunnah ya ce Davido a wurin Musulmi ya koyi hada sallah da barkwanci.

Ya ce a Arewacin Najeriya sau da dama zaka ga Musulmai suna barkwanci da sallah, me yasa ba za a rufe kofar barnar ba kafin wadancan su dauka.

Ya ce:

"Tsakanin mu da Allah, a nan Arewa ana samun 'yan barkwanci da sallah ko ba a samu?.

Kara karanta wannan

Yadda Marigayi Albani Ya Hango Janye Tallafin Man Fetur Shekaru 9 da Suka Wuce

"Ba ka sha ganin barkwanci ba ana salla ga liman wani ya zo ya birkita shi ya fara karatu bai gama ba ya gudu ya bar sallar?.
"Dan Allah ya aka yi Musulmai 'yan nan suka mai da sallah abin barkwanci, al'umma ba ta dauki irin wannan mataki ba?.
"Idan su sunyi irin wannan su wa suka bude musu kofa su yi haka?."

Mallam Idris Abdallah Idris a bangarensa ya ce hakan cin mutuncin Musulunci ne, duk Musulmi ya kamata ya ji rashin dadin hakan.

Hakan cin zarafi ne na addinin Musulunci

Ya ce:

"Wannan cin zarafin Musulunci ne kuma duk Musulmi ya kamata ya ji ba dadi.
"Shi kuma za a kira shi da ya tuba da ba da hakuri idan ya yi wannan tunda dan Adam ne sai a yafe masa idan har an amince da tubansa."

Yayin da Mallam Muhammad Adam ya ce wannan ba komai ba ne a wurin Yarbawa don su hakan ba komai ba ne a dabi'arsu.

Kara karanta wannan

Ya Saduda: Davido Ya Yi Abin Da Ya Dace Bayan Goge Faifan Bidiyon, Saura Abu Daya Tak

Ya ce babu wani mataki da Musulmi za su dauka a kai duk da abu ne na batanci amma dai hakan aikata sabo ne a addinance.

A Karshe, Davido Ya Goge Faifan Bidiyon Rashin Da'a Ga Musulunci Da Ake Ta Cece-kuce

A wani labarin, mawaki Davido ya ji korafin jama'a ya goge faifan bidiyon da ake ta cece-kuce a kai.

Mutane da dama dai musamman a Arewacin Najeriya sun soki mawakin inda suka bukaci ya goge tare da ba da hakuri.

Jarumi Ali Nuhu da Sanata Shehu Sani da kuma Bashir Ahmad na daga cikin wadanda suka yi martani akan bidiyon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel