Abba Gida Gida Ya Yi Sababbin Nade-Naden Mukamai 15 a Jihar Kano

Abba Gida Gida Ya Yi Sababbin Nade-Naden Mukamai 15 a Jihar Kano

  • A farkon makon Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin shugabannin hukumomin gwamnatin Kano
  • Mai girma Gwamnan jihar Kano ya fitar da sanarwa ta ofishin Babban sakataren yada labaransa a dazu
  • Sanusi Dawakin Tofa ya ce a wadanda aka ba mukamai akwai Dr. Indabawa da Dr. Abubakar Minjibir

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - A ranar Litinin, 7 ga watan Agusta 2023, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da nadin wasu shugabannn hukumomin gwamnatin jihar Kano.

Sakataren yada labarai na gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bada sanarwar a wani jawabi na musamman da ya fitar a shafinsa.

Nade-naden shugabannin da aka yi ya kunshi hukumomin kula da alkaluma da cibiyar koyon kasuwanci ta Aliko Dangote da wasu makarantu.

Kano: Abba Kabir Yusuf
Gwaman Kano, Abba Kabir Yusufa taron NGF: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Farfesa Aliyu Isa Aliyu ya samu matsayi

Farfesa Aliyu Isa Aliyu wanda malamin lissafi ne a jami’ar tarayya ta Dutse ya samu matsayi.

Kara karanta wannan

Lamari Ya Yi Kamari, Tinubu Ya Zauna da Gwamnonin da ke Iyaka da Jamhuriyyar Nijar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin mukaman da aka raba

1. Hon. Kabiru Getso Haruna – Babban shugaban hukumar tallafawa dalibai.

2. Farfesa Aliyu Isa Aliyu – Darekta Janar na hukumar alkaluma ta Kano.

3. Dr. Kabiru Ado Zakirai – Babban shugaban hukumar kula da makarantun sakandare (KSSMB)

4. Hon. Alkasim Hussain Wudil – Shugaban cibiyar koyon sana’a ta Aliko Dangote

5. Farouq Abdu Sumaila – Shugaban hukumar jagoranci da bada shawara.

6. Alh. Umar Shehu Minjibir - Shugaban hukumar kula da aikin gwamnati a Kano.

7. CP Kabiru Muhammad Gwarzo mai ritaya – Darekta Janar na cibiyar tsaro, Gabasawa.

8. Dr. Abdullahi Garba Ali – Darektan makarantar Informatics, Kura.

9. Hajia Shema'u Aliyu – Darekta cibiyar harkar tarbar baki.

10. Dr. Musa Sa'ad Muhammad- Darektan cibiyar wasanni, Karfi.

11. Dr. Abubakar Shehu Minjibir – Darektan cibiyar cigaban aikin jarida.

12. Abdullahi S. Abdulkadir – Darektan cibiyar aikin gonawa, Kadawa.

13. Jazuli Muhammad Bichi – Darektan cibiyar dabbobi, Gargai.

Kara karanta wannan

Maryam Shetty: ‘Yan Siyasa, ‘Yan Takara Da Mutane 5 Da Suka Ga Samu Da Rashi

14. Dr. Maigari Indabawa – Darektan cibiyar harkar fina-finai, Tiga.

15. Kabiru Yusuf – Darektan cibiyar harkar kifi, Bagauda.

Sanarwar ta ce duka wadanda aka nada za su karbi ragamar aiki nan da sa’o’i 48. Abin da hakan yake nufi shi ne za su shiga ofis zuwa ranar Laraba.

Gwamna ya fito da karin Hadimai

A wata sanarwar dabam, an ji Mai girma Gwamnan ya kara nada wasu masu bada shawara:

1. Hon. Garba Dirbunde

2. Hon. Wakili Aliyu Garko

3. Air Commodore Yusha'u Salisu Tudunwada Wada mai ritaya

4. Hon. Musa Ado Tsamiya

5. Gwani Musa Falaki

6. Dr. Sulaiman Wali Sani Mni,

7. Farfesa Auwalu Arzai

8. Hon. Ahmad Sawaba

9. Alh. Tajuddeen Gambo

10. Hon. Baba Abubakar Umar

Hadiman za su rika ba Gwamna shawara a kan harkokin ilmi, makarantun ‘yan kasuwa, tsaro, lambatu, harkokin addini da kula da gandun jeji.

Abdullahi Umar Ganduje ya kama aiki

Idan aka koma siyasar kasa, za a ji labari ‘yan PDP za su rude da Abdullahi Umar Ganduje ya yi zama da Sanata Anyim Pius Anyim a garin Abuja.

Jigon na PDP kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya ziyarci shugaban jam’iyyar APC a jiya, hakan ya kara jawo rade-radin sauya-sheka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel