Maryam Shetty: ‘Yan Siyasa, ‘Yan Takara Da Mutane 5 Da Suka Ga Samu Da Rashi

Maryam Shetty: ‘Yan Siyasa, ‘Yan Takara Da Mutane 5 Da Suka Ga Samu Da Rashi

  • Kusan ko ina a Najeriya, surutu ake yi a game da Maryam Shetty, wata ‘yar siyasa daga Jihar Kano
  • Daga lokacin da aka bada sunanta domin zama Minista zuwa sa’ilin da aka cire ta, ake ta maganganu
  • Kafin wannan Baiwar Allah, akwai ‘yan siyasa da-dama da su ka rasa kujera su na daf da hawa kai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Rahoton Daily Trust ya tattaro wasu daga cikin ‘yan siyasar da su samu irin wannan kaddara, ga jerin nan kamar haka:

Maryam Shetty
Maryam Shetty, Machina da Price Audu Hoto: The Cable, All Africa, Imranmuhdz
Asali: UGC

1. Mukhtar Shehu Idris – Bello Matawalle

Da aka yi zaben Gwamna a Zamfara a 2019, Mukhtar Shehu Idris ya samu fiye da 60% na kuri’un da aka kada, don haka INEC ta tabbatar da nasararsa.

A karshe kuwa kotun koli a karkashin Mai shari’a Tanko Muhammad, ta tabbatar da cewa APC ba ta shirya zabe gwani ba, aka ba PDP mulkin jihar.

Kara karanta wannan

Ganduje Sun Yi Wa Maryam Shetty Izgili a Bidiyo Bayan ‘Tunbuke’ Ta a Jerin Ministoci

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

2. David Lyon - Douye Diri

A 2020 kuwa kotun koli ta fatattaki David Lyon ne ana gobe zai zama Gwamna. Mary Odili ta umarci a karbe masa satifiket, a damkawa Dauyo Diri.

Dalilin wannan hukunci shi ne abokin takarar Lyon a APC, Biobarakuma Degi-Eremienyo ya yi karyar takardu, ya mikawa INEC satifiket na bogi.

3. Prince Abubakar Audu – Yahaya Bello

Prince Abubakar Audu ya sha gaban Gwamna Idris Wada a zaben jihar Kogi a 2015, jam’iyyar APC ta kama hanyar nasara da ratar kuri’u 41,353.

Jaridar ta ce ana tsakiyar zaben Abubakar Audu ya rasu, INEC kuma ta sake gudanar da zabe a wasu wurare, karshe Yahaya Bello ya samu mulki.

4. Bashir Sheriff Machina - Ahmad Lawan

A zaben tsaida gwani na Sanatan Yobe ta Arewa, Bashir Sheriff Machina ya samu tikitin APC, yayin da Ahmad Lawan ya tafi harin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Kano: Muhimman Abubuwa 5 Da Ba Ku Sani Ba Game Da Maryam Shetty Da Tinubu Ya Sauya Sunanta A Jerin Ministoci

INEC ta karbi sunan Machina a jerin ‘yan takaran 2023, kuma da farko kotu ta tabbatar da haka. A karshe Lawan yake kan wannan kujera a yau.

5. Maryam Shettima - Mariya Mahmud Bunkure

Kun ji labari siyasar Jihar Kano ta na daukar wani fasali na dabam bayan Bola Ahmed Tinubu ya dare kan mulki da aka zo nada Ministocin gwamnati.

Wani fai-fen bidiyo ya tona Abdullahi Ganduje da mai dakinsa da Mariya Mahmoud Bunkure da wasu mata su na gulmar Maryam Shetty bayan cire sunanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel