Lamari Ya Yi Kamari, Tinubu Ya Zauna da Gwamnonin da ke Iyaka da Jamhuriyyar Nijar

Lamari Ya Yi Kamari, Tinubu Ya Zauna da Gwamnonin da ke Iyaka da Jamhuriyyar Nijar

  • Bola Ahmed Tinubu ya kira wasu Gwamnonin Arewa domin tattauna halin da Nijar ta ke ciki a yau
  • Kusan duk wani Gwamna da jiharsa ta ke makwabtaka da kasar Nijar ya halarci wannan zama a jiya
  • Ba a san wainar da aka toya ba, amma bai rasa nasaba da yadda za a magance matsalar a ruwan sanyi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi zama na musamman da wasu gwamnonin jihohi kan batun halin da kasar Nijar ta ke ciki.

A wata sanarwa daga bakin mai taimaka masa, Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya sa labule da gwamnonin da jihohinsu ke iyaka da kasar Nijar.

Ku na sane cewa jihohin da su ke makwabtaka da Nijar sun hada da Sokoto, Jigawa, Borno da Yobe. Ragowar jihohin dai su ne Kebbi sai Katsina.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Majalisa Ba Ta Tabbatar da El-Rufa'i Ba, Ta Amince da Mutum 45

Gwamna
Gwamnoni masu alaka da Jamhuriyyar Nijar Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hotuna sun fito

Olusegun Dada ya fitar da hotunan zaman Bola Tinubu da Alhaji Ahmed Aliyu (Sokoto), Umar Namadi (Jigawa) da Mai Malam Buni (Yobe).

Idris Nasir (Kebbi) da Dr Dikko Radda Umaru (Katsina) sun halarci taron da aka yi a Aso Rock. Da alama Gwamnan Borno bai samu halarta ba.

Rahoton da aka samu daga tashar Arise ya ce taron yana cikin kokarin da shugaban kasar Najeriya yake ni na magance rikicin shugabancin makwabtan.

Ana fatan samun mafita ta lalama

Gwamnatin Bola Tinubu ta na neman yadda za a samu mafita a sakamakon hambarar da gwamnatin Mohammed Bazoum da aka yi kwanaki.

An yi zaman Lahadin ne jim kadan bayan majalisar dattawa ta ba gwamnatin kasar shawarar ta nemi yadda za a sasanta ba tare da harba bindiga ba.

Kara karanta wannan

Ahir dinka: PDP ta ja kunnen Tinubu, ta ce kada ma ya fara yakar Nijar, ga dalili

Da su ka yi zama a ranar Asabar, Sanatoci sun nuna ba su goyon bayan Tinubu wanda ya zama shugaban kungiyar ECOWAS ya jawo yaki a yankin.

Lokaci ya na neman ya kure

Rahoton jaridar Sun ya ce an yi taron ne a wani wuri da ake kira ‘Glass House’, inda shugaban kasa ya kan zauna na wucin gadi a fadarsa ta Aso Villa.

Zuwa yanzu wa’adin da kungiyar kasashen yammacin Afrika su ka ba sojojin da su ka yi juyin mulki a Nijar ya gabato ba tare da sun sallama mulki ba.

Matsayin Sheikh Yabo a Sokoto

Jawabin Bello Yabo ya nuna cewa juyin mulkin da aka yi, maganar cikin gidan Nijar ne ba na mu ba, iyakar Bola Tinubu bada shawara ba katsalandan ba.

Malaman ya ce babu bambanci tsakanin Nijar da Sokoto, duk ‘yanuwa ne, ya ce idan dai Sojojin Najeriya su na da karfi, su yaki ‘yan ta’addan Najeriya ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel