Hazikan matasa 3 da suka ci gajiyar tsarin Kwankwasiyya sun yi fice a Duniyar kimiyya

Hazikan matasa 3 da suka ci gajiyar tsarin Kwankwasiyya sun yi fice a Duniyar kimiyya

  • Aliyu Isa Aliyu, Tukur Abdulkadir Sulaiman, da Abdullahi Yusuf sun amfana da tsarin Kwankwasiyya
  • Gwamnatin Rabiu Kwankwaso ta tura wadannan mutane domin su karo karatu a jami’o’in kasashen waje
  • Yanzu dukkansu sun kammala PhD a bangaren lissafi, sun zama hukumomin kansu a jerin masanan Duniya

Jigawa - Wasu mutane uku da suka amfana da tsarin Kwankwasiyya na tura matasa zuwa makarantun kasashen waje sun yi suna yanzu a Duniya.

Daily Nigerian ta rahoto cewa wadannan masana; Aliyu Isa Aliyu, Tukur Abdulkadir Sulaiman, da Abdullahi Yusuf su na cikin wadanda ake ji da su a yau.

Dr. Aliyu Isa Aliyu, Dr. Tukur Abdulkadir Sulaiman, da Dr. Abdullahi Yusuf su na cikin masana 2% da aka fi yawan kafa hujja da dogara da binciken da suka yi.

Kara karanta wannan

Garkuwa da mutane: Dakarun ‘Yan Sanda sun kubutar da mutum kusan 100 daga jejin Zamfara

Wadannan matasan masana sun ci gajiyar tsarin da Rabiu Musa Kwankwaso ya fito da shi a lokacin ya na gwamna, aka kai su karo ilmi a jami’o’in ketare.

Sun zama malamai a jami'ar FUD

A shekarar 2012 suka je jami’ar fasaha ta Irbid da ke kasar Jordan, suka yi digirinsu na biyu. Yanzu dukkansu su na koyarwa ne a jami’ar FUD, Dutse-Jigawa.

A watan Agustan 2021 ne wasu masana a karkashin jagorancin Farfesa John Loannidis da ke jami’ar Stanford, California, kasar Amurka suka yi wannan aiki.

Hazikan matasa 3
Dr. Aliyu Isa Aliyu, Dr. Tukur Abdulkadir Sulaiman, da Dr. Abdullahi Yusuf Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Farfesa John Loannidis da mutanensa sun yi amfani da rumbun SCOPUS, suka gano masana kimiyyar da aka fi bibiya da dogara da irin binciken da suka yi.

Solacebase tace an tattaro masana da masu nazari sama da 100, 000 a wannan jeri daga cikin masana kimiyya miliyan takwas a fannonin ilmi 22 da aka zakulo.

Kara karanta wannan

Kwara: PDP ta kori mambobinta su 4 sannan ta dakatar da wasu 5 saboda sabawa jam’iyyar

Su wanene wadannan malamai?

1. Dr. Abdullahi Yusuf

Abdullahi Yusuf haifaffen garin Dala ne a jihar Kano, ya yi karatun ilmin lissafi a jami’ar fasaha da ke Wudil.

A shekarar 2019 ne Yusuf ya kammala digirinsa na PhD a ilmin lissafi a jami’ar Elazig, kasar Turkiyya.

2. Dr. Tukur Abdulkadir Sulaiman

Rahoton yace shi kuma Tukur Abdulkadir Sulaiman mutumin Kiru ne, ya yi digirin farko a jami’ar Bayero.

Shi ma ya kammala digirinsa na PhD a lissafi a jami’ar Firat da ke garin Elazig, kasar Turkiyya, duk a 2019.

3. Dr. Aliyu Isa Aliyu

Na ukunsu, Aliyu Isa Aliyu ya fito ne daga garin Bichi, ya yi digirin B.Sc a lissafi a jami’ar Bayero a Kano.

A shekarar 2018, Aliyu ya samu shaidar PhD a bangaren lissafi a jami’ar Firat, Elazig ta kasar Turkiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel