Cire Tallafi: Masu Biredi Sun Shirya Kara Farashi Saboda Tsadar Fulawa, Sun Ce Hakan Ya Zama Dole

Cire Tallafi: Masu Biredi Sun Shirya Kara Farashi Saboda Tsadar Fulawa, Sun Ce Hakan Ya Zama Dole

  • Kungiyar masu yin biredi a Najeriya (PBAN) sun shirya kara farashin biredi saboda cire tallafin mai a kasar
  • Shugaban kungiyar, Emmanuel Onuorah shi ya bayyana haka yayin hira da 'yan jaridu inda ya ce ba su da zabi
  • Ya ce kara farashin ya zama dole ganin yadda kayayyakin hada biredin duk shigo da su ake daga ketare

FCT, Abuja - Yayin da farashin kayan abinci ke kara hauhawa, masu siyar da biredi sun shirya kara farashinsu saboda yanayin tattalin arziki.

Masu biredin suka ce hakan ya zama dole ganin yadda aka cire tallafin mai a kasar da farashin Naira kasuwanni, Legit.ng ta tattaro.

Masu biredi sun shirya kara farashi saboda tsadar fulawa
Masu Siyar Da Biredi Na Shirin Kara Farashi. Hoto: Bloomberg / Contributor.
Asali: Getty Images

Shugaban kungiyar masu yin biredi a Najeriya (PBAN) Injiniya Emmanuel Onuorah shi ya bayyana haka yayin ganawa da jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya Ta Sha Alwashin Kakaba Wa Dalibai Harshen China A Jami'o'i, Ta Roki Alfarma

Masu biredin suka ce hakan ya zama dole ganin yadda aka cire tallafi

Ya ce mafi yawan kayayyakin da ake hada biredin shigo da su ake yi Najeriya wanda hakan ya ke da alaka da farashin Naira a kasuwanni.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Mafi yawan kayayyakin da muke amfani da su wurin yin biredin shigo da su ake Najeriya.
"Saboda haka dole farashin zai karu ganin yadda gwamnatin Tarayya ta mayar da Naira ta yi yawo a kasuwanni, yadda babban bankin kasar ba shi da iko akan farashin.
"Masu siyar da fulawa suna amfani da wannan dama na farashin Naira don kara kudin, hakan zai sa farashin biredi ya karu a bangaren mu.
"Karin farashin biredin kuma zai kawo cikas a cinikayya wanda hakan zai sa gidajen biredi da dama kullewa."

Ya ce matakin da Tinubu bai dace ba

Kara karanta wannan

"Tsadar Tumatir": Mata a Abuja Sun Koma Amfani Da Karas Don Yin Miya

Akan cire tallafi kuwa, Emmanuel ya ce hakan bai yi tsari ba ganin yadda gwamnatin ta cire ba tare da kawo wani tsari da zai tallafawa 'yan kasuwa ba.

Ya ce:

"Wannan mataki a ganinmu bai dace ba, ganin yadda babu wani tsari kafin cire tallafin da zai taimaki 'yan kasuwa da sauran 'yan kasa.
"Mafi yawan ma'akatan mu ba sa iya biyan kudin sufuri zuwa wurin aiki wanda hakan ke kawo cikas a harkar yin biredin."

Hauhawar farashin kaya ya karu da 15.63% a Najeriya

A wani labarin, hauhawan farashin kaya sai kara tashi ya ke a Najeriya musamman kayan masarufi.

Bincike ya tabbatar da cewa farashin kaya ya karu da kashi 15.63 a watan Disamba ta 2021.

Hukumar kididdiga ta NBS ce ta bayyana hakan a rahoton da ta fitar a ranar Litinin, 17 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.