Mata a Abuja Sun Koma Amfani Da Karas Wajen Yin Miya Yayin Da Tumatir Ya Yi Tashin Gwauron Zabi

Mata a Abuja Sun Koma Amfani Da Karas Wajen Yin Miya Yayin Da Tumatir Ya Yi Tashin Gwauron Zabi

  • Mata a babban birnin tarayya sun koma amfani karas da wasu kayayyakin lambu wajen yin miya saɓanin tumatir
  • Hakan dai ya samo asali ne daga tashin gwauron zabi da tumatir ya yi a cikin 'yan kwanakin nan
  • An alaƙanta tsadar tumatirin da tsadar taki da kuma yanayin yadda ake nomansa a Najeriya

Abuja - Wasu mata a babban birnin tarayya Abuja, sun daina amfani da tumatir wajen yin miya sakamon tashin gwauro zabin farashin da ya yi.

Matan sun shaidawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa sun koma amfani da wasu abubuwan irinsu karas, gauta, kabewa da sauran wasu kayayyakin lambu wajen yin miya.

Mata sun koma amfani da karas wajen yin miya a Abuja
Mata sun koma yin miyar da karas da gauta a Abuja saboda tsadar tumatir. Hoto: Rabiu Biyora / Lafiya Uwar Jiki
Asali: Facebook

Mata suna amfani da gauta wajen yi miya saɓanin tumatir

Wata mata mai suna Jummai Amodu, ta bayyana cewa sakamakon tsadar da tumatir ya yi, ta koma amfani da gauta wajen yin miyar da suke cin shinkafa ita da yaranta biyar, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Mercy Aigbe Ta Bayyana Darasin Da Ta Koya A Saudiyya Yayin Aikin Hajji, Bidiyon Da Ta Saki Ya Dauki Hankulan Mutane

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce sun kasance kusan kullum suna cin shinkafa da miya ita da yaran na ta.

A cewarta:

“Tun da tumatur ya yi tsada, sai na yanke shawarar fara amfani da gauta wajen yin miya, kuma yana da daɗi kamar tumatur.”
“Bambancin da ke tsakanin miyar gauta da ta tumatur shi ne launinsu. Ina kuma amfani da miyar kabewa wajen ci da shinkafa, duk da yake tana da ɗanɗanonta na musamman, tana da daɗin ci da shinkafa sosai.”

Misis Helen Omo, wata ‘yar kasuwa, ta ce duk da cewa tumatir na da matukar muhimmanci a kusan dukkan gidaje a Najeriya, ƙarancinsa ya sa wasu ‘yan Najeriya tunanin wasu hanyoyin na daban.

Ta ƙara da cewa ta je kasuwa domin sayo tumatirin da za ta yi miya, wanda a baya farashinsa ba ya wuce N2000 zuwa N2500, yanzu a kan N6500 ake siyar da shi.

Kara karanta wannan

“Kamar a Fim”: Matashiya Ta Auri Hadadden Dan Koriya a Asiya, Hadadden Bidiyon Bikin Ya Zautar Da Yan Mata

Mista Chinedu, wani dan kasuwa ya shaidawa NAN cewa yana jin daɗin cin shinkafa da miyar tarugu ko da farar miya.

A cewarsa:

“Farashin duka kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi, amma na tumatur ya wuce gona da iri, ba mamaki saboda yanzu ba lokacin tumatur ba ne.”
"Baya ga tsada da ya yi, ya kuma yi ƙaranci sosai, wanda sakamakon hakan ne yasa muka yanke shawarar amfani da wani abun daban."

Yan kasuwar tumatir sun koka kan ƙarancin ciniki

Wani mai sayar da tumatur mai suna Umar Adamu a kasuwar Nyanya, ya ce ya daina sayar da tumatur na wasu kwanaki saboda karancin masu saye.

Ya ce mutane ba sa zuwa su sayi tumatirin saboda muguwar tsadar da ya yi.

Misis Rukayya Umar, babbar jami’ar Abraks Farm Produce Nigeria Limited, ta ce babban dalilin da ya sa tumatir ya yi ƙaranci shi ne tsadar taki.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Shiga Yanayi Bayan Saurayinta Ya Gudu Saboda An Yanke Mata Kafa

A cewarta, manoma da dama ba sa noman shi saboda ba sa iya siyen takin zamani, inda ta ce taki na da matukar muhimmanci wajen noman tumatir.

Rukkaya ta kuma ce dogaro da noman rani kaɗai na ɗaya daga cikin dalilan da suka haifar da karancin tumatirin.

NAN ta ruwaito cewa babban kwandon tumatur da ake siyar da shi a kan kusan Naira 10,000 a baya, yanzu ana sayar da shi ne kusan N35,000 yayin da manyan kwandunan suke wuce wannan farashin.

Farfesa ya shawarci 'yan Najeriya sun rungumi kiwon kwaɗi saboda tsadar kifi

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan wani malamin makaranta, Farfesa Moshood Mustapha da ya shawarci 'yan Najeriya su rungumi kiwon kwaɗi domin haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasa.

Farfesan ya bayyana hakan ne a yayin wata lakca a Ilorin babban birnin jihar Kwara a ranar 8 ga watan Yunin da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel