FG Ta Yi Alkawarin Kakaba Yaren China A Tsangayoyin Jami'o'in Najeriya, Ta Bayyana Alfanun Hakan

FG Ta Yi Alkawarin Kakaba Yaren China A Tsangayoyin Jami'o'in Najeriya, Ta Bayyana Alfanun Hakan

  • Gwamnatin Tarayya ta jaddada aniyarta na inganta harshen China a jami'o'in Najeriya don koyawa dalibai
  • Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume shi ya bayyana haka a yau Litinin 3 ga watan Yuli a Abuja
  • Jakadan kasar China, Cui Jianchun ya ce a shirye suke don taimakon Najeriya ta fannin kasuwanci da noma

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta na kirkirar tsangayar koyan harshen China a jami'o'in Najeriya.

Gwamnatin ta tabbatar wa kasar China cewa ta shirya don inganta mu'amala mai karfi tsakanin kasashen biyu.

FG ta yi alkawarin kawo yaren China jami'o'in Najeriya
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume. Hoto: Facebook.
Asali: Facebook

Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume shi ya bayyana haka yayin karbar bakoncin jakadan China, Cui Jianchun a yau Litinin 3 ga watan Yuli a Abuja, Vanguard ta tattaro.

Najeriya ta bayyana shirinta don kara dankon zumunci da China

Kara karanta wannan

FG Na Fuskantar Matsin Lamba Yayin da Aka Nemi Ta Dokubo Kan Barazanar Da Ya Yi Wa Inyamurai

A wata sanarwa daga ofishinsa, Akume ya ce Najeriya na jin dadin mu'amala da China a bangarorin ayyuka da kasuwanci da noma da sauransu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya roki China da ta saka hannun jari a kasar don ba wa sabuwar gwamnatin daman cika burinta na kawo ci gaba.

A cewarsa:

"Ina son in godewa China yadda ta zuba hannun jari don inganta mana kasa wanda muke karbar bashi na kudade da muka saka su a harkokin sufuri.
"Bambancin a bayyane ya ke, muna tsammanin za ku sake zuba kudade, na yi imanin yanzu da harkar kasuwanci kuka zo.
"Duk wani taimako daga wurinku zai mana amfani, saboda yadda wannan gwamnati ke son yin aiki sosai, muna tsammanin taimakon ku daga lokaci zuwa lokaci.

Najeriya ta bayyana shirinta na kirkirar tsangayar koyon harshen China

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Mutane 6 Sun Rasu a Borno Yayin Da Wani Bam Da 'Yan Boko Haram Suka Binne a Kan Hanya Ya Tashi

"Muna godiya da yadda kuke ba wa daliban Najeriya tallafin karatu wanda wasu sun kammala karatun, ba za ku yi danasani ba, kafin wani lokaci 'yan Najeriya sun fara yaren China.
"Mun shirya don kirkirar tsangayar koyan yaren China a jami'o'in Najeriya wanda za a na koyawa dalibai."

China ta shirya taimakon gwamnatin Tinubu don inganta rayuwar 'yan kasar

Tun farko a jawabinsa, jakadan kasar China, Cui Jianchun ya tabbatar da aniyar gwamnatin China na ba da gudunmawa ga gwamnatin Tinubu don ci gaba da aikin alkairi.

Ya ce China a shirye take don yin aiki tare da gwamnatin Tinubu da kuma inganta mu'amala tsakanin kasashen biyu, cewar tahotanni.

Shugaba Tinubu Ya Nada Tsohon Ministan Buhari, George Akume Matsayin SGF

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya nada George Akume a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya.

George Akume ya kasance shi ne tsohon ministan ayyuka na musamman a tsohuwar gwamnatin Buhari.

Kara karanta wannan

Limaman Kiristoci A Arewacin Najeriya Sun Yi Allah Wadai Da Kona Alkur'ani A Sweden, Sun Bayyana Mataki Na Gaba

Kafin zama minista a tsohuwar gwamnatin, Akume ya mulki jihar Benue a matsayin Gwamna har wa'adi biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel