Fetur Ya Haura N300 a Gidajen Mai Daga Jin Bola Tinubu Ya Sanar da Janye Tallafi

Fetur Ya Haura N300 a Gidajen Mai Daga Jin Bola Tinubu Ya Sanar da Janye Tallafi

  • Farashin man fetur ya fara lulawa sama tun kafin Bola Ahmed Tinubu ya shiga fadar Aso Rock
  • Jawabin sabon shugaban kasar Najeriya ya jawo wasu ‘yan kasuwa sun kara kudin mai da 100%
  • Tinubu ya ce an wuce zaman tallafin fetur, hakan zai yi sanadiyyar a daina saida mai a kan N210

Abuja - Abubuwa sun canza a gidajen mai mintuna kadan bayan an rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa na 16 a Najeriya.

Vanguard ta ce farashin man fetur ya tashi a wurare da-dama a sakamakon jawabin da sabon shugaban Najeriya ya yi a kan tsarin tallafin mai.

Tun kafin ya shiga ofishin shugaban kasa a Aso Rock, Bola Ahmed Tinubu ya nuna gwamnatinsa ba za ta cigaba da biyan tallafin man fetur ba.

Kara karanta wannan

Tinubu: Muhimman Abubuwa 7 da Aka Tsakura Daga Jawabin Sabon Shugaban Kasa

Gidan mai
Gidan mai ana saifa fetur Hoto: Getty
Asali: Getty Images

Hakan ya jawo wasu masu motocin haya a Najeriya su ka fara kara kudin mota a safiyar rantsuwar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tinubu ya tabbatar da zamanin biyan ‘yan kasuwa tallafi domin fetur ya yi araha ya wuce, kafin yanzu ana saida lita tsakanin N195 da N220.

Karin 100% a Abuja, Legas

Jaridar ta ce gidajen mai da-dama a Legas sun nunka farashinsu da 100% a nan-take, wasunsu sun koma saida litar kowane fetur a kan N370.

A babban birnin tarayya Abuja inda aka rantsar da Tinubu, an koma gidan jiya na dogon layi.

A gidajen man Conoil da Adova a yankin Karu, lita ta na nan a N195 amma akwai dogon layi, a wasu wuraren sai mutum ya biya N315 ko N370.

"Na tanadi mai na"

Legit.ng Hausa ta fahimci kafin a je ko ina layi ya fara yawa a wasu gidajen mai a Zariya. A wasu gidajen kuwa, kwatsam aka daina saida fetur.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Sanar da Nade-Naden Mukamai 7 Ana Tsakiyar Rantsar da Tinubu

Wani ‘dan kasuwa a Kano ya shaida mana cewa tun ana shirin rantsar da sabuwar gwamnati ya tafi gidan mai, ya cika tankin abubuwan hawansa.

Mutane su na tsoron tashin da mai zai yi, zai iya jawo abubuwa su yi tsada sosai a fadin kasar.

Wani da ‘yan jaridan su ka samu a gidan mai ya fara kuka da gwamnati tun yanzu, ya zargi Tinubu da fara azabtar da al’umma daga karbar mulki.

Dama an fadawa al'umma

Tun a makon jiya aka ji labari Kashim Shettima ya ja-kunnen ‘Yan Najeriya, ya ce gwamnatinsu za ta fara da gargada a ofis, amma za a murmure.

Zababben mataimakin shugaban kasar ya ce Gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu za tayi fama da tsarin tallafin man fetur da farashin Dala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel